Mutum uku sun mutu sannan daruruwan suka jikkata bayan sake fashewar wasu na’urori da Hezbollah ke amfani da su wajen sadarwa a Lebanon, kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Fashewar ta afku ne a a gidajen jama’a a wajen Birnin Beirut da Garin Sohmar da kuma Kudancin kasar.
- Xi Ya Jaddada Ba Da Cikakkiyar Dama Ga Fa’idar Siyasa Ta CPPCC
- Yunƙurin Sayar Da Jariri, Ƴansanda Sun Damƙe Mutane 2 A Legas
An garzaya da mutanen da suka jikkata zuwa asibiti a babban Birnin kasar.
Har ila yau, wani dan jarida ya bayyana cewa mutum biyu sun jikkata bayan fashewar na’ura a Kauyen Ali al-Nahri da ke tsakiyar Bekaa.
Wani shaida ma ya ce an samu fashewa a cikin wani mota kusa da wata makabarta a Birnin Jdeidet Marjeyoun.
Wani rahoto ya nuna cewa jami’an leÆ™en asirin Isra’ila, Mossad ne suka dasa ababan fashewa a dubban na’urar sadarwa ta Hezbollah kafin sun fashe a faÉ—in Æ™asar Lebanon.
Wata majiya daga manyan jami’an tsaron Lebanon ta shaida wa Reuters cewa an shigo da na’urorin sadarwar ne a watan da ya gabata zuwa Lebanon.
Majiyoyi daga Isra’ila da Amurka sun ce Isra’ila ta tayar da ababan fashewar ne a na’urorin tun kafin lokacin da aka tsara za su tashi bisa tsoron cewa Hezbollah ta gano abin da aka kitsa.
Aƙalla mutum tara ne suka mutu sannan dubbai suka jikkata sakamakon fashewar.
Wani Æ™wararre kan makamai ya shaida wa BBC cewa akwai yiwuwar an dasa ababan fashewa masu nauyin giram 20 a na’urar.
Lamarin ya zo wa mutane da dama ba shiri ba tsammani kamar yadda masu sharhi a kan harkokin tsaro a Gabas ta Tsakiya suka bayyana wa BBC.
Rahotanni na nuna cewa mutum tara sun mutu, sannan kusan mutum 3,000 sun jikkita, inda daga ciki kuma akwai aÆ™alla 200 da suka ji munanan raunuka, kamar yadda Ministan Lafiyar Al’umma na Lebanon, Firass Abiad ya bayyana, inda ya Æ™ara da cewa yawancin raunukan a hannuwa da fuskoki ne.