Uwargidan shugaban kasa, Misis Remi Tinubu, ta bayar da gudummawar Naira miliyan 40 tare da kayayyakin abinci daban-daban ga wadanda fashewar tankar mai ta afkama wa a kauyen Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Wata tawaga karkashin jagorancin uwargidan kakakin majalisar wakilai, Hajiya Fatima Tajudeen Abbas ce ta mika tallafin a madadin Misis Remi Tinubu a fadar gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar.
Da take mika cak da kayan abinci ga uwargidan gwamnan jihar, Hadiza Umar Namadi, uwargidan shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Busola Kukoyi, ta fitar a ranar Alhamis, ta ce, tana jajantawa wadanda iftila’in ya shafa.
Da yake karbar gaisuwar ta’aziyya da gudunmawa daga uwargidan shugaban kasa Tinubu tare da godiya, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya tabbatar wa tawagar cewa, za a raba wannan tallafin cikin adalci ga wadanda lamarin ya shafa.
Har ila yau, ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan yadda ya gaggauta daukar mataki a matsayinsa na Uba, gwamnan ya bayyana cewa, wadanda abin ya shafa da ke samun kulawar likitoci, suna samun sauki.
Tun da farko dai, tawagar ta kai ziyara a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya na Rasheed Shekoni da ke Dutse, inda a halin yanzu wasu daga cikin wadanda abin ya shafa ke samun kulawar likitoci a Asibitin.