• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fashin Baki Kan Kasafin Kudin 2025 Na Naira Tiriliyan 54.99

by Abubakar Abba and Sulaiman
7 months ago
Kasafin kudi

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da baban kasafin kudin kasar wanda ya kai yawan Naira tiriliyan 54.99, daidai da karin kaso 56.89 daga kasafin kudi na Naira tiriliyan 35.05 na shekarar 2024, wanda kuma ya hada har da wani sabon karin Naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin kudin.

Kasafin kudin na shekarar 2025, kusan za a iya cewa, shi ne, babba da aka taba yi a cikin shekaru 65 da suka wuce a kasar.

Shugaban kasa Bola Tinubu a lokacin gabatar da kasafin a yayin zaman hadaka da majalisun kasar suka yi, yawa kasafin lakabi da na saita tattalin arzikin kasar da kuma kara bunkasa shi.

Kazalika, gwamnatin ta sanya burin yin amfani da ksafin wajen kara samar da kayan aiki, kara tabbatar da tsaro da samar da shirye-shiyen jin kan alumma.

Amma abin tambaya shi ne, duba da yadda ake ci gaba da samun raguwar kudaden shiga, bin dimbin bashin da ake yiwa kasar, shi gwamnatin za ta iya cimma burin kashe kudade don wanzar da wadannan shirye-shiyen da take son cimma ?

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida

Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho

Bubu da kari, abin mahimmancin shi ne, shi talakan Nijeriya zai iya gani a kas na irin wadannan shirye-shiyen da gwamnatin ke son aiwatarwa?

 

Fannin Da Gwamnatin Za Ta Zuba Kudaden:

A kasafin kudin na 2025, Gwamnatin Tarayya ta warewa bangaren tsaro Naira tiriliyan 6.11 wanda ya kai ta samar da karin kaso 88 daga cikin kasafin kudin da ta warewa fannin na Naira tiriliyan 3.25 a 2024.

Shin wannan burin na Gwamnatin zai iya cika, duba da yadda aka gaza dakile ta’addanci, ‘yan fashin daji, wanda idan ba a mayar da hankali ba, a 2025, tarihi ne zai sake mai-maita kansa.

An ware Naira tiriliyan 5.99 a cikin kasafin kudin don yin tituna, gadoji da kuma manyan ayyuka a babbar hanyar da ta tashi daga Legas zuwa Kalaba da ta Sokoto zuwa Badagry, inda aka samu karin da ya kai sama da kaso 350 sabanin Naira tirliyan 1.32 da aka ware a kasafin kudin bara.

Idan har da a gudanar da wadannan ayyukan, za su kara samar da ayyukan yi da habaka kasuwanci.

Bugu da kari, a kasafin kudin na 2025, an warewa ilimi, kiwon lafiya da bunkasa hazaka Naira biliyan 5.7 wanda ya kai kaso 161, sabanin Naira tiriliyan 2.18 da aka ware a kasafin kudi na 2024, inda fannin aikin noma ya samu Naira tiriliayan 3.73, wanda hakan ya nuna an samu kari mai yawa da ya zarta na Naira biliyan 362, inda an yin wannan karin ne, don a karya farashin kayan abinci a kasar.

 

Sai dai, shin ko wannan karin kudaden zai samar wa talakawan kasar sauki?

Amma wasu kwararu a Cibiyar Tsare-Tsare Da Bincike Kan Tattalin Arzikin Kasa (CEPR) ta yi nuni da cewa, idan har ba a wanzar da kuma kara kudi a cikin kasafin kudi hakan ba zai yi tasiri ba.

 

Kara Yawan Karbo Rancen Kudade:

Kudin ruwan da bashin da Gwamnatin ke biya ya lakume Naira tirilaya 16.3, wanda ya kai kaso 98, inda hakan ya nuna an samu karin Naira 8.25 a kasafin kudi na 2024.

Sai dai, wani babban kalubalen shi ne, yadda Nijeriya ke biyan bashin kudin ruwa na bashin da ta karbo fiye da wanda rake son kashewa a bangarorin ilimi, kiwon lafiya da samar da kayan aiki.

Gwamnatin ta yi hasahsne kudaden shiga da take son samu za su karu daga Naira tiriliyan18.32 zuwa Naira 36.35 trillion, wadanda suka kai karin kaso 123.19, musamman ta hayar tara haraji da zuba hannun jari na ketare.

Duba da yadda a arihin Nijeriya ka gaza tara kudaden shigar da ake sa ran tarawa, wasu kwararru a taron kungiyar tattalin arziki Nijeriya (NESG) sun yi garadin cewa, bai mai yuwa banen wadannan hasashen da aka yi su tabbata ba.

Kasafin kudin kasar ya rubanya a cikin shekara daya, amma duk da haka kudaden shigar kasar sun yi rauni.

Alal misali, a cikin kasafin kudin na 2025, ‘yan Majalisa sun samu karin Naira biliyan 344.85, wanda a kasafin kudi na 2024, suka samu karin Naira biliyan 197.93, inda kuma su ke son ‘yan kasar su kara jan damarar ci gaba da kula da rayuwarsu.

Bugu da kari, ‘yan Malasira Dokoki sun sun samawar da kansu karin sma da Naira biliyan 7 na kudaden sun a tafiye-tafiye, da kuma wasu dimbin kudaden da suka warewa kansu na jin dadi da na biyan kafafen ‘yada labarai.

A shirye-shiyen jin kan alumma, an ware Naira biliyan 723.68 kacal wanda aka kara kudin zuwa Naira biliyan 600, amma duk da haka, wani dan bangare kadan ne, aka kashe kan ayyukan gwamnatin.

Akwai dai dimbin buri da aka sanya a cikin kasafin kudin na 2025, wanda duk da wannan burin, cin abinci sauku a rana, na neman gagarar talakan kasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

sallah
Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida

October 11, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho
Tattalin Arziki

Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 
Tattalin Arziki

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Next Post
Ba Gwamna Bala Ne Ya Soke Hawan Daushe Ba – Masarautar Bauchi Ta Bayyana Gaskiya

Ba Gwamna Bala Ne Ya Soke Hawan Daushe Ba – Masarautar Bauchi Ta Bayyana Gaskiya

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025
Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

October 13, 2025
NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

October 13, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

October 13, 2025
Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

October 13, 2025
Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

October 13, 2025
Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba

Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba

October 13, 2025
Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano

Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.