Akwai kyakkyawar alaka tsakanin tattalin arzikin Australiya da tattalin arzikin kasar Sin, inda Sin ta dauki kusan kashi daya bisa uku na dukkan kayayyakin ficen Australiya a shekarar 2023, sa’annan hajojin Sin sun kai sama da kashi daya bisa hudu na kayayyakin shigen Australia. Don jaddada muhimmancin dangantakar, firaministan Australiya Anthony Albanese ya bayyana a wannan shekarar cewa, “daya cikin hudu na ayyukan yi a Australiya ya dogara ne a kan kasuwanci, kuma daya cikin hudu na dalar da Australiya ke samu na kayayyakin fice daga cinikayya ce da kasar Sin.”
Australiya ta kasance cikin koma bayan tattalin arziki na kan kowanne mutum wato per capital a shekarar 2023. Ma’ana, yayin da tattalin arzikinta ke ci gaba da bunkasa, yawan al’ummarta na karuwa da sauri fiye da tattalin arzikin. A halin yanzu tattaunawa kan tattalin arzikin kasar ta fi mai da hankali kan matsalar tsadar rayuwa, yayin da karin talakawan Australiya ke bukatar abinci mai yawa, da gidaje da kudaden amfani wadanda ke tasiri ga rayuwar yau da kullun a kasar.
- Alamomi 20 Na Ciwon Kansa Da Suka Kamata A Sani
- Manzon Musamman Na Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Afrika ta Kudu
Bisa wadannan dalilan ne Australiya take fatan ingantuwar dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin za ta haifar da wani fa’ida ta fuskar tattalin arziki don taimakawa magance wadannan yanayi. Muhimmin aiki ga bangarorin biyu zai kasance nemo hanyoyin zurfafa dangantakar cinikayya, da kirkirar sabbin hanyoyin hadin gwiwa, a fannin habaka ababen hawa na lantarki (EV) a Australiya, saboda kasar Sin ita ce kan gaba a duniya a fasahar EV, tana da kuma masana’antu wadanda suka yi matukar dacewa da matsayin Australiya a matsayin kasa mafi girma wajen samar da lithium a duniya. Yayin da kasashen biyu suka kuduri aniyar aiwatar da manufofin rage hayakin carbon mai gurbata muhalli, ba abin mamaki ba ne cewa wani bangare na ziyarar firaministan kasar Li ya hada da ziyarar jihar yammacin Australiya wadda ta mai da hankali kan hakar ma’adinai.
Ziyarar ta firaminista Li kuma ta zo a daidai lokacin da amincewar jama’ar Australiya ga Amurka ta ragu matuka, inda wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar Lowy ta gudanar a baya-bayan nan ta nuna cewa kashi 56 cikin 100 na jama’ar Australiya ne kawai suka amince da Amurka wajen yin abin da ya dace idan aka kwatanta da kashi 61 cikin 100 na bara. Wannan wata alama ce da ke nuna cewa al’ummar Australiya na fahimtar hakikanin fa’idar dunkulewar kasashen duniya, saboda haka, bukatar aiwatar da manufofin ketare mai cin gashin kanta, na tabbatar da alakar aiki tsakanin Australiya da kasar Sin ya zama wani muhimmin bangare.