Rundunar ‘yansandan Jihar Gombe ta ceto jarirai uku tare da cafke wasu mutane 16 da ake zargi da laifin safarar yara a jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Mahid Abubakar, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin kwamishinan ‘yansandan jihar, Hayatu Usman a Gombe a ranar Laraba.
- CBN Ya Nada Sabbin Shugabannin Gudanarwar Wasu Bankuna
- Bangaren Layin Dogo Na Sin Ya Yi Jigilar Fasinjoji Mafi Yawa A 2023
Abubakar, ya ce an shigar karar ne a karshen mako biyo bayan rahoton sirri da aka samu daga mutanen yankin Barunde na Jihar Gombe.
Ya ce an ceto jarirai uku daga hannun wadanda ake zargin, yayin da wasu biyu kuma aka yi safarar su daga jihar.
A cewarsa, daya daga cikin jariran da aka yi safarar su a yanzu yana Legas, yayin da dayan kuma an ceto shi a Anambra.
Ya bayyana cewa ana kokarin kwato sauran jariran biyu da kuma mayar da su jihar.
Abubakar, ya bayyana cewa, yayin bincike, an gano cewa an sayar da daya daga cikin jariran kan Naira 400,000.
Ya ce an sayar da jaririn ga wani mutum a jihar tare da hadin gwiwar wani ma’aikaci a jihar.
A cewar kakakin rundunar ‘yansandan, rundunar ta samu rahoton sirri kan daya daga cikin iyayen da suka sayar da dansu ga wadanda ake zargin.
“Wannan wani laifi ne na hada baki da fataucin yara inda aka kama wata Khadija Manzo da wasu 15 bayan rahoton sirri da aka samu daga al’ummar Barundde a karshen mako.
“A wani lokaci a shekarar da ta gabata, wata Khadija Manzo da wasu 15 sun shiga harkar sayar da jarirai.
“Da samun rahoton, jami’an tsaro na Lowcost Division sun gudanar da bincike wanda ya kai ga kama Manzo, da sauran wadanda ake zargi,” in ji shi.
Abubakar ya ce bincike ya nuna cewa Manzo ya sayar da jarirai biyu ga Ukamaka Ugwu a lokuta daban-daban.
Ya ce an kama wasu da ake zargi da hannu wajen aikata laifin.
Da yake karin bayani, Abubakar ya ce: “Bincike ya nuna cewa ta sayar da wani jariri kan Naira 400,000 ga wata Tina Raphael.
“Kuma ta bayar da Naira 200,000 ga wani Haruna Abubakar, wanda ke aiki da gwamnatin Gombe.
“Yahaya Suleiman ya karbi Naira 200,000 daga hannun ta ya bai wa Haruna Abubakar.
“Ukamaka Ugwu ya sayi yara biyu daya a halin yanzu yana Legas daya kuma a Anambra, amma ‘yansanda na kokarin ganin an dawo da jariran.”
Abubakar ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.