Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, ya bukaci shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da ya fito fili ya fada wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ainihin halin da ake ciki a APC, ba bayanin da yake samu a cikin fadar shugaban kasa ba.
Fayemi wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), ya yi wannan kira ne ga Ganduje a yayin kaddamar da wani littafi mai suna “Yadda APC ke gudanar da siyasarta”, wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa na yankin Arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman ya rubuta, da ya gudana a Abuja.
- Kamfanonin Jamus 22 Za Su Zuba Jarin Fam Biliyan 3 A Nijeriya
- Kwankwaso A Sikeli Bayan Hukuncin Kotun Koli
Taron ya samu halartar fitattun jagororin jam’iyyar APC da suka hada da Ganduje da tsaffin shugabannin jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da Cif Bisi Akande da wakilan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da na shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa da sauransu.
Fayemi ya ce, “Na yi farin ciki da shugaban jam’iyyarmu ya zo wannan wuri. Wannan jam’iyyar bai kamata ta zama ‘yar kallo ba wajen tsara manufofin gwamnati. Ya kamata jam’iyya ta zama ita ce za ta tsara manufofin gwamnati. Ya kamata wannan gwamnati da dinga bin manufofin jam’iyya wajen aiwatar da tsare-tsarenta wadanda suka dace domin kawo wa al’umma sauki, ba wai abin da shugaban kasa yake ji a fadar shugaban kasa ba.
“Dukkanmu mun taba rike mukamin gwamnati kuma mun san yadda al’amura suke. Na yi farin ciki da shugabanmu ya tabbatar da cewa zai karanta wannan littafin. Kamata ya yi ya zama wajibi a karanta wa dukkan ‘ya’yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC da shugabanni a matakin jiha da na unguwanni domin mu fara aikin sake gina jam’iyyarmu wadda na yi imanin Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai jajirce a kai.”
A nasa jawabin, Ganduje ya ce jam’iyyar APC na bukatar a samar da tsari mai kyau tare da mayar da hankali wajen biyan bukatun al’ummar Nijeriya.