Kwalejin Kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin tarayya da ke Bauchi (Fedpoly) ta sassanya na’urorin ɗaukan hotuna na zamani (CCTV) a wasu zaɓaɓɓun ɗakunan zana jarabawa domin daƙile matsalolin satar Jarabawa da kuma inganta harkokin tsaro a cikin makarantar.
Shugaban kwalejin, Alhaji Sani Usman, shi ne ya shaida hakan sa’ilin da ke ganawa da ‘yan jarida a ranar Lahadi bayan da tawagar bin sawun kwasa-kwasan da aka sahale na 2025 na National Board for Technical Education (NBTE) suka ziyarci kwalejin.
- Kamun Akanta-janar Take-taken Toshe Bakin Gwamnan Bauchi Ne – Ƙungiya
- Gwamnan Bauchi Ya Yi Alhanin Rasuwar Shaikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi
Ya ce, “Mun samar da sanya na’urorin Kemarori a muhimman azuzuwan karatun, sannan an wata manyan hol-hol ɗinmu da na’urar samar da hasken rana domin tabbatar da ana samun wuta a kowani lokaci.
“Bugu da ƙari, mun kammala shirin binciken karatu wanda TETFund ta tallafa na tsawon shekaru biyu da suka gabata, wanda zai ba mu damar faɗaɗa samar da na’urar CCTV a ciki da wajen ɗaukan karatunmu.”
A faɗinsa, shirin wani yunƙuri ne na magance matsalolin satar jarabawa da duk wani shiri na janyo kalubale ga tsaro a cikin kwalejin.
Da ya ke magana kan ziyarar tawatar NBTE, Rector ɗin ya ce aikin sahalewa na da matuƙar muhimmanci domin gano irin ƙoƙari da azamar makaranta a cikin shekaru biyar da suka gabata da nufin tabbatar kayan koya da koyarwa da malamai suna nan kan tsarin da aka amince da tafiyar da su tun da farko.
Ya tabbatar da cewa kwasa-kwasai har guda 78 ne jami’an NBTE suka nazarta a yayin wannan ziyararz, “Tawagar sun gama aikin su na ziyarar, yanzu haka muna zaman jiran sakamakon bincike da bin sawun nasu ne,” ya ƙara shaida.
A nata ɓangaren, Dakta Fatima Umar, daraktan shirye-shiryen kwalejoji kuma jagorar tawagar na NBTE, ta buƙaci kwalejin Kimiyya da fasaha na gwamantin tarayya da ke Bauchi da ya maida hankali wajen magance matsalolin gine-gine da kuma giɓin ma’aikata.
Da take samun wakilcin Adesina Oluade, ta jero sauran matsalolin da ta gano kamar ƙarancin littafai na ɗalibi, mujallu na ilimi, rashin samar da wutar lantarki yadda ya kamata, inda ta ce bangarorin na buƙatar daukan matakan gaggawa.
Umar ta jaddada cewa tsarin sahalewa na da nufin ƙarfafa tabbatar da samar da ilimi mai ingancin da kyautata aiki, inda ta sha alwashin cewa kwamitin zai cigaba da yin gaskiya da adalci a yayin aikinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp