Hukumar kula da lafiyar tituna da gyara su ta tarayya (FERMA) reshen Jihar Kebbi ta kammala ayyukan tituna guda 14 da aka ware wa jihar a karkashin ayyukan rabon jari na 2021 da kyautata zamantakewa al’umma a jihohin kasar nan.
Injiniya mai kula da hukumar a jihar Alhaji Rilwanu Usman, ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, ya ce an hanzarta kammala ayyukan ne bisa la’akari da mahimmancin tattalin arziki na amfanin noman da al’ummar jihar ke gudanar wa a yankinsu domin saukaka musu jigika da zirga-zirgan amfanin gona.
Ya ke cewa: “Ayyukan da aka kammala a karkashin kasafin kudi sun hada da gyare-gyare na musamman na titin Kebbi zuwa Kontagora a kan titin Malando-Ngaski-Warra a Jihar. Ayyukan gyare-gyare ne na musamman da suka hada da cike ramuka, cika wasu sassan titin da kwalta da sauransu, kuma an kammala shi a watan Fabrairu.
“Mun yi aikin gyaran kan iyakar Sakkwato da titin Argungu-Birnin Kebbi, wanda ya hada da gyaran bangon siminti a cikin garin Gotomo inda gefe ke barazanar yanke hanyar. Haka kuma an kammala gyaran kafadun hanya a kusa da Zauro-Ambursa, da sauransu, duk an kammala su a watan Fabrairu,” ya shaida.
Ya cigaba da cewa, “Mun yi titin kwalta mai tsawon kilomita 2.7 tare da gina magudanan ruwa mai nisan kilomita 1.7 a Jega G.R.A kuma an kammala su a watan Maris na bana. Har ila yau, akwai aikin da muka yi a mazabar Koko-Maiyama na tarayya inda aka gina titin kasa mai tsawon kilomita 1.5 da magudanan ruwa guda biyar a Karaye- Sabon Kamba da Sabon Sara.
“Maganar zababbun hanyoyi ta hanyar daidaitawa inda wani sashe gefe a garin Gotomo ke haddasa asarar rayuka da dama kuma muka shiga tsakani muka daidaita.”
Injiniya Rilwanu Usman ya kara da cewa akwai kuma ayyuka guda biyar a fadin kananan hukumomin uku na jihar da ke karkashin ayyukan kulawa na musamman. “An yi gyaran hanyar Argungu-Bui mai tsawon mita 550 da ya lalace. Ayyukan gyaran na musamman na hanyar Tuga-Ka’oje, an gyara wani bangare na titin da ya gaza, wanda ya hada da ramuka, gina magudanan ruwa, da sauran su, duk an kammala su a bana.
“Haka zalika mun kammala aikin titin Malando-Ngaski-Warra mai tsawon 480, tare da ba da takardar shaida na sashin da ba a yi nasara ba tare da gyara kwalta da facin ramuka baya ga wadda ke karkashin babban aikin. An yi gyaran hanyar Masama-Aljannare-Duroci da ke karkashin gundumar Kebbi ta arewa, da magudanar ruwa da titin mita 180 da kwalta.
Kazalika “An yi ayyukan gyaran sassan da suka lalace a kan iyakar Birnin Kebbi zuwa Argungu, an gyara kafadu mai tsawon mita 600, sannan an yi gyaran ramuka mai fadin murabba’in mita 487 tsakanin kan iyakar Kebbi da Sakkwato. Akwai ƙarin ayyuka na yau da kullun a karkashin kasafin kudi na 2022 a cikin jihar.
“Akwai gyaran titunan da ke tsakanin ramukan kilomita 18 zuwa 38 da ke kan hanyar Argungu zuwa Bui da ake yi a kai-a kai. 749.2 na sassan da suka gaza fiye da murabba’in 400 an yi faci. Aayyukan da aka yi a kai a kai, an yi gyare-gyare gadan-gadan a kan titin Kalgo-Bunza da Feka, an kuma gyara kafadu mai tsawon kilomita 1.2 a kowane wuri, sannan kuma an yi gyaran wasu ramuka 490.
“Akwai kuma gina titin 1.22, magudanar ruwa da magudanan ruwa guda uku a Jega phase 2 G.R.A baya ga titin kwalta mai tsawon kilomita 2.7 a karkashin aikin tarayya.
“A kokarin da wasu ‘yan majalisa suka yi, mun sanya fitulun na’ura masu aiki da hasken rana da dama a wasu manyan garuruwa, kuma ana ci gaba da aikin gina magudanun ruwa da sauran ayyukan hanyoyi da dai sauransu,” in ji Injiniya Rilwanu Usman.
Daga karshe yaba wa hukumar FERMA da ‘yan majalisar dokoki da Atoni-Janar na kasa Abubakar Malami da Gwamna Atiku Bagudu bisa kokarinsu na ganin jihar ta kasance cikin na gaba wajen kula da hanyoyin tarayya a kasar nan.