Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari shawara, Ismaeel Ahmed, ya bayyana fitar Malam Nasir El-Rufai daga jam’iyyar APC a matsayin babban rashi ga jam’iyyar.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ahmed ya jero manyan gudunmawar da El-Rufai ya bayar, ciki har da rawar da ya taka wajen haɗa CPC da ACN, shawo kan Buhari ya sake tsayawa takara a 2015.
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria
- Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto
Ya nuna takaicinsa kan fitar El-Rufai daga jam’iyyar, inda ya ce ya yi tsammanin shugabannin APC za su hana hakan faruwa.
Duk da rashin jituwarsa da suke samu a wasu lokuta, Ahmed ya yaba wa El-Rufai tare da masa fatan alheri.
El-Rufai ya fice daga APC tare da sauya sheƙa zuwa SDP a ranar Litinin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp