Hukumar kwallon kafa ta Argentina (AFA) ta sanar da dakatar da golan ƙasar da ya lashe gasar cin kofin duniya, Emiliano Martinez wasanni biyu da FIFA ta yi.
An samu ɗan wasan na Aston Villa mai shekaru 32 da laifin “keta ƙa’idojin wasa mai kyau” a ɓangarori biyu daban-daban, an samu Martinez da keta ƙa’idojin hukumar ta FIFA lokacin da yake rike da kofin Copa America a kwuiɓinsa bayan wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Argentina ta doke ƙasar Chile a ranar 5 ga watan Satumba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Martinez ya yi irin wannan aikin ba, a baya ma ya yi hakan da kyautar safar hannu ta zinare da aka ba shi, bayan Argentina ta doke Faransa a bugun fanariti a gasar cin kofin duniya ta 2022.
Hukumar kwallon ƙafa ta duniya FIFA ta kuma saka masa takunkumi saboda ya bugi kyamarar mai ɗaukar hoto ta TV da safar hannu bayan da suka doke Colombia da ci 2-1 a ranar 10 ga watan Satumba.
Hukumar ta AFA ta bayyana rashin gamsuwarta da hukuncin na FIFA ta yanke, inda ita hukumar kwallon ƙafa ta Argentina ta nuna rashin amincewarta da matakin da kwamitin ladabtarwa na FIFA ya ɗauka,” in ji sanarwar.
Sakamakon yanke wannan hukunci Martinez kuma babban dan wasa a tawagar Argentina ba zai buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Venezuela a ranar 10 ga Oktoba ba, da wasan Bolivia a ranar 15 ga Oktoba ba.