Allah ta’ala ya fada a wata Aya cikin Suratul Bakra, “Haka nan muka sanya ku al’umma ce zababbu adalai don ku zama masu shaida ga mutane (shaida ga annabawa idan mutanensu sun karyata su), wannan Ma’aiki kuma zai zamo maishaida gare ku (al’ummarsa)”
Abul Hasanil Kadisi ya ce, Allah ya bayyana fifikon Annabi (SAW) da fifikon al’ummarsa da wannan aya.
Haka Allah ya sake fada a wata aya game da falalar al’ummarsa (SAW) cewa “ya ku wadanda kuka yi Imani ku dinga yin ruku’u, ku dinga yin sujuda (ma’ana ku yi sallah) ku bauta wa Ubangiji, ku dinga yin aikin alkhairi (duk abin da ya kasance kishiyar sharri, to sunansa alkhairi) ko za ku rabbanta. Ku yi Jihadi (Kokari) cikin daukaka kalmar Allah matukar Kokari, Allah ne fa ya zabe ku, Allah bai sanya muku kunci a cikin addini ba; addininku irin addinin Babanku (Annabi) Ibrahim, Allah ne ya ambace ku (da sunan) Musulmi tun gabannin saukar Alkur’anin nan da kuma a cikinsa don Annabi (SAW) ya zama maishaida a gare ku, ku kuma ku zama shaida ga sauran mutanen da suka zo kafin ku, ku tsaida sallah; ku ba da zakkah, ku yi riko da Allah shi ne mai taimakon ku, madalla da mai taimako; madalla da mai ba da agaji (Allah)”.
Ba yaki ne kawai Jihadi ba, yaki shi ne karshen abin da ake fassara Jihadi da shi. Kamar yadda duk mutumin da aka yi wa tiyata ko yanke wani sashe na jikinsa; dole ce tasa aka yi masa hakan saboda an rasa wasu hanyoyin da za a bi a samu lafiyar. Fita salloli da yin su cikin jam’i Jihadi ne musamman sallar Asubahi. Manzon Allah (SAW) ya ce yaki karamin abu ne. Kisa aba ce mai sauki fiye da dagewa wajen fita yin sallolin farilla a cikin jam’i.
Musulunci abu ne mai taushi da dadi, babu kausasawa da tsanantawa, duk wanda kuma ya tsananta a ciki; a bashi lokaci kadan abin zai buwaye shi. Manzon Allah (SAW) ya ce addinin nan (Musulunci) mai karfi ne, duk wanda ya shiga da tsanani addinin zai kada shi. Don haka mu dinga saukakawa kar mu tsananta. Mu dinga bishara; kar mu dinga kore mutane daga falala da samun rahamar Allah (SWT).
Allah Tabaraka Wata’ala yana sa taushi da girmamawa idan zai yi magana da Annabi Muhammadu (SAW). Ana iya gane irin wannan tausasawar ta yadda idan da wani ne daga cikin Annabawa Allah zai yi maganar da shi akwai dan kausasawa ko fada a ciki. Dukkan Annabawa Bayin Allah ne har da Annabi (SAW), Allah zai yi yadda ya ga dama da su amma kuma a janibin Annabi (SAW) sai a ji Allah yana tausasa masa magana.
Yana daga tausasa maganar da Allah ya yiwa Annabi (SAW), a cikin Alkur’ani Allah ya ce, “Allah ya yafe maka, me ya sa ka yi musu izini (cewa su zauna)”. Za a tafi Yakin Tabuka sai munafukai suka zo wurin Annabi (SAW) ya yi musu afuwa kar su tafi Yakin, sai Annabi (SAW) ya karbi uzurinsu saboda Allah ya bashi zabi a kan hakan. Allah Ta’ala ya ce, “idan suka nemi izininka cikin wani sashe na sha’aninsu; ka yi wa wanda ka ga dama a cikinsu”. To sai ya yi musu uzuri su zauna a gida kar su tafi Yakin, shi ne sai Allah yake ce masa Allah ya yafe maka amma me ya sa ka yi musu uzuri kar su tafi yakin. A karshen ayar Allah ya ce “ai da ka jira har sai masu gaskiya (muminai) sun bayyana gare ka kuma ka san su wanene ke karya (munafukai). A cikin ayar, Allah ya fara ambaton maganar yafiya tukuna kafin daga bisani ya ce wa Annabi (SAW) don me ya yiwa mutanen uzuri domin kar Annabi (SAW) ya ji a cikin ransa cewa ko ya yi wa Allah laifi ne da ya yi hakan.
Abu Muhammadul Makiyy ya ce, an ce “Allah ya yafe maka” din nan da aka fara kawowa bude magana ce, tana da matsayi ne da ma’ana ta “Allah ya kubutar da kai”. Kamar al’adace ta irin yadda mutane ke yi a farko idan za su yi magana. Misali, idan mutane za su yi magana da wani babba a cikinsu, kamar Larabawa suna farawa da wata magana ta girmamawa kamar su ce “Allah ya kubutar da kai ko Allah ya girmama ka”. Hausawa suna da irin wannan, za ka ji idan sun je wurin wani babba kamar Malami haka, kafin su fara magana za su ce “Allah gafarta malam”, kuma suna fadar hakan ne ba domin sun ga malamin ya yi wani laifi ba, sai dai sun fada ne don girmama shi. Idan Basarake ne za su ce “Ranka shi dade”, idan babban ma’aikaci ne su ce “Yallabai” da sauran su. To watakila saboda irin wannan ka’ida ce sai Allah Ta’ala ya fara wa Manzon Allah maganar da cewa “Allah ya yafe maka”.
Malam Aunu da Ibn Abdullah sun ce ma’anar ayar, Allah (SWT) ya baiwa Annabi (SAW) labari ne na rangwamen da ya yi masa kafin ya shaida masa abin da ya yi na barin aikata mafificin abu, ma’ana da ya bar wannan abin bai yi ba; da hakan ya fi. Idan Allah ya raba maganar zunubi ga Annabawa ba zunubi ne irin yadda muke tunani ba, a’a, a wurinsu ana ce wa abin ‘tarku aula’ ma’ana abin nan da suka aikata da sun bar shi ba su yi ba; da hakan ya fi. Hausawa kan ce “akan bar halas don kunya”, ka ga ai ba wai don halas din babu kyau ba ne ya sa aka bari, sai dai barin abin ya fi zama kamala suke nufi.
Wata rana wani ya tambayi Shehu Ibrahim Inyass (RA) cewa “Shehu mece ce ma’anar ayar da ta ce “Adamu ya sabi Ubagngijinsa”? Sai Shehu ya ce masa “Yadda ka ji ta din nan haka take, amma fa ka sani Allah Ubangijin Annabi Adamu (AS) ne, zai iya fada masa abin da ya ga dama. Amma da ni da kai a karkashin Annabi Adamu (AS) muke, shi shugabanmu ne, don haka ba za mu iya fada masa haka ba”. Domin fitar da wannan ma’anar a fili, kamar Misali mutum ne yana da baba da kaka, sai babansa ya yiwa kakansa laifi, mutumin yana zaune sai kakan ya aike shi wurin baban nan nasa ya ce masa “je ka kira mun ubanka mutumin banza ya yi mun laifi”, to shi wannan mutumin tunda kakansa uba ne a wurin babansa ai idan ya je ba zai fadi irin yadda kakan ya fadi ba ya ce ma babansa “mutumin banza” kamar yadda kakan ya fada, sai dai ya ce “baba, kaka yana kiran ka”. Don haka su Annabawa ba irin zunubinmu ne suke yi ba, a’a ‘tarku aula’ ne nasu. To ita ma wannan ayar da ta ce wa Manzon Allah don me ya yi wa mutanen nan uzuri? Ba tana nufin Manzon Allah ya yi laifi ba ne, a’a ya bar mafificin abu ne.
Malam Samarkandi ya ruwaito daga wani sashe na malamai cewa ma’anar ayar ta “Allah ya yafe ma, me ya sa ka yi masu izini” tana nufin “Allah ya kubutar da kai ya mai tsarkakakken zuciya”. Sai ya kara da cewa da Allah ya fara da cewa “don me ka yi masa uzuri” da an ji tsoron kar zuciyarsa ta tsage saboda yadda yake tsoron Allah. A lokacin da Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW) “ka tsaya kamar yadda aka umurce ka” sai ga farin gashi (furfura) ya fito masa a kai. Shi ya sa wanda ya fi sanin Allah ya fi jin tsoron Allah. Annabawa sun fi kowa sanin Allah, don haka sun fi jin tsoron Allah. Shi ya sa idan Sarautar Allah ta motsa, Annabawa sun fi jin tsoro har da Shugaban Halitta baki daya Manzon Allah (SAW).
To da Allah Ta’ala ya fara da maganar “me ya sa ka yi musu uzuri?”, da zuciyarsa ta kece saboda kwarjinin wannan maganar, sai dai cewa Allah (SWT) bisa rahamarsa sai ya fara ba Manzon Allah (SAW) labari da yafewa har zuciyarsa ta natsu; sannan daga baya ya ce masa don me ka yi musu izini cewa su zauna a gida, da ka bari har sai mai gaskiya ya bayyana maka a cikin hanzarin daga makaryaci.
A cikin wannan bayani, duk wani mai hankali zai fahimci cewa Manzon Allah (SAW) yana da girman matsayi a wurin Allah saboda sai da Allah ya fara fadar yafiya tukuna kafin tambayar sa cewa me ya sa ya yi musu uzuri.
Yana daga girmamawar Allah ga Manzon Allah (SAW) da alherinsa ga Annabi, mutum ko shi wane ne bai isa ya gane iyakar matsayin Annabi a wurin Allah ba, wanda ya ce zai yi haka ma sai dai jijiyar rayuwarsa ta yanke. Malam Misdawaihi (Malamin Nahawu) ya ce Malamai sun tafi kan cewa an yiwa Manzon Allah (SAW) rarauka ne da wannan ayar ta “Allah ya yafe ma, me ya sa ka yi musu izini”, domin Allah ya kiyaye Annabi (SAW) ya aikata wani abu da Allah ba ya so ballantana har ya yi masa fada (SWT). Ayar tana nufin zabi ne aka ba Annabi (kuma Ummul Mu’umina Aisha (RA) ta ce idan aka bashi zabi kan wani abu yana zabar mafi sauki) shi ya sa ya yi ma wadanda suka nemi zama a gida izini. Ayar kuma tana bayyana cewa Allah yana baiwa Annabi labari ne kan cewa koda ma bai yi musu izinin ba; ba za su je yakin ba saboda munafuncinsu. Don haka babu laifin da ya aikata cikin izinin da ya yi musu. A wata ayar ma Allah ya ce da (munafukan) sun fita yakain; za su hada rigima a can saboda akwai wadanda suka wakilta suna musu leken asiri.