Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kaddamar da wata runduna ta musamman da za ta yi yaki da bata-gari da ke kashe-kashen rayuka da barnata dukiyoyin jama’a a Jihar Filato.
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun wanda ya kai ziyarar gani da ido kan asarar rayuka da dama a wasu kananan hukumomin Jihar Filato, ya ce rundunar ta musamman da gwamnatin tarayya ta amince da kaddamarwa a jihohi 10 na Nijeriya, za ta fara aiki ne nan take a Jihar Filato.
- Sabuwar Shekara: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Yi Wa Fursunoni 39 Afuwa A Gombe
- Hare-Hare: Gwamnatin Filato Ta Ayyana Zaman Makokin Mako Guda
Tuni da mataimakin Sufeto-Janar na shiya ta hudu, Ebong Eyibio ya kaddamar da jami’an runduna ta musamman zuwa yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaron.
A ci gaba da neman mafita kan batun kalubalen tsaron, Sanata mai wakiltar tsakiyar Filato, Diket Plang ya gabatar da wasu batutuwa a gaban majalisar dattawa, inda ya ce za su taimaka wajen kawo zaman lafiya a jihar.
Sanata Diket Plang ya koka kan yadda maharan su 400 suka ratsa wurare suka mamaye kauyuka fiye da 20 ba tare da wani ya gansu ba.
Ya kuma koka kan yadda wasu ke mamaye gonaki da gidajen wadanda suka yi gudun hijira, tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da jami’an tsaro na dindindin a yankunan.
A cewar Dah Mai’anguwa, Jamok Mafwalal Machambe daga gundumar Butura a karamar hukumar Bokkos, sun yi na’am da zuwan jami’an tsaron, ya kuma bukaci jama’a su basu goyon baya don samar da tsaro.
Sakataren kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Barkin Ladi, Abubakar Gambo yace suna bukatar jami’an tsaron su yi adalci.
A makon da ya gabata ne wasu mahara suka hallaka mutane sama da 160 a wasu kauyuka sama da 20, lamarin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin ‘yan Nijeriya.