Shugabar kula da Tashoshin Jiragen Sama na kasa Olubunmi Kuku ya sanar da cewa, tashoshin Jiragen Sama na jihar Legas wato Murtala Muhammed da na Abuja Nnamdi Azikiwe da na Abuja, sun samu sahalewar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA).
Hukumar ce ta bayyana haka a cikin sakon da ta wallafa a shafinta D a ranar Juma’ar data gabata
- Jirgin Ruwan Aikin Jiyya Na “Peace Ark” Ya Kammala Aikinsa A Benin
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Kaddamar Da Jirgin Ruwa Mai Aikin Nazari A Teku Mai Zurfi
Kuku a lokacin gabatar da shedar amincewar da aka gudanar a Abuja ta ce, tun a 2020, ba a bayar da takardun iznin ba.
Ta sanar da cewa, samun wannan nasarar ta kasance a matsayin matakan kara inganta ayyukun hukumar.
A cewarta, har yanzu akwai abuwan da ya katama a gudanr a hanyoyin tashi da saukr Jiragen, musamman sanya fitilun haskaka hanyoyin domin su kai daidai da na duniya.
Ta sanar da cewa, a shirye muke domin mu magance wadannan kalubalen, inda ta bayar da tabbacin cewa, za a zuba kudade domin kara ainganta aikin.
Kuku ta kuma jinjinawa shugaba Bola Tinubu da ministan sufurin Jiragen sama Festus Keyamo, a kan taimakaon da suka bayar na kammala wannan aikin na sahalewar.
Mukaddashin Darakta Janar na riko a NCAA Chris Najomo a na sa jawabin a wajen taron ya sanar da cewa, a watan Maris na 2001, ne aka amince da sabon tsarin na ICAO.
Ya sanar da cewa, an amince da bukatar yin sabon tsarin na zamani an fara amfani da shi ne a ranar 27 ga watan Nuwambar 2023 wadda kuma Nijeriya, ta bi wannan ka’aidar tare da amincewa wadannan tashoshin Jiragen saman biyu a 2017.