Fina-finai masana’antar shirya fina-finai ta Kudanci wato Nollywood sun shahara wajen maida hankali kan labarai na soyayya. Amma a ‘yan shekarun baya-bayan nan lamarin ya fara sauyawa.
Misali kamar fina-finan 2018 King of Boys, 2018 Lionheart, 2019 The Set Up, 2020 Who’s the Boss da kuma 2021 Dwindle, dukka labaran da fina-finan suka koyar ba a kan batu na soyayya ba ne, sun yi ne a kan karfin iko-mulki, koyar da mata sana’o’in dogaro da kai da kuma abokanta.
Hakan kila bai rasa nasa da halin da ake ciki a rayuwar yau ta kasar nan wanda ke nuni da cewa muddin mutum in bai da nashi to rayuwa ka iya zama masa mai wuya, hatta ga dogara da wani ta fuskancin tattalin arziki na iya zama abun damuwa ga al’umma.
Don haka fina-finan sun yi kokarin nusar da al’ummar Nijeriya muhimmancin tsayuwa da kafafu da kuma neman abun yi domin samun kudi da kuma yadda mutum zai ririta kudaden da ke shigo masa domin rayuwar gaba ta kyau.
A wannan lokacin, mun gano fina-finan Nollywood da suke koyar da mu darussan da suka shafi rayuwa, soyayya da kuma kudi. Ba kamar da baya ba da suke maida hankali kan labarai na soyayya zallah ko suke bai wa soyayyar fifiko sosai.
Wadannan fina-finai da suka fito za mu iya daukan darasi daga fim din ‘The Smart Money Women’ wanda aka yi a shekarar 2020 da kuma ‘Chief Daddy’ da aka yi a 2018, wadannan wasan kwaikwayo na barkwancin za su iya zama misali wajen koyar da mu kan sana’a da samun kudi.
Bisa hakan ga wasu fina-finai guda biyar da suke koyar da mu game da kudi da muhimmancisa da yadda ake samunsa.
The Smart Money Woman (2020)
Wani fim ne da aka gina labarinsa kan yadda mata za su zama masu wayo da hikima a bangaren hulda da kudade ko inganta sha’anin kudinsu. Wasan kwaikwayon ya koyar da masu kallo sha’anin da suka shafi kudade, kama daga kashe kudade, basuka, matakan tanadi da kuma zuba hannun jari.
Darurrusan da ke cikin labarin fim din:
Fim din ya koyar da yadda mata za su samu ilimin ririta kudadensu. Akwai darurussa sosai da fim din ya koyar amma bar mu jero kadan daga ciki.
1) Fim din ya koyar da mata yadda za su san kimar kudinsu da daraja shi a kashin kansu. (Sanin me za ki iya saya da meye ba za ki iya saye ba);
2) Neman ragi ko sauki don guje wa sayen kayayyaki da tsada);
3) Ki zama mai wayo a kan kudinki (Kada ki amince da bude asusun ajiyar banki na hadaka ke da fakiri ko wacce ba ta da aikin yi);
4) Idan kina da sana’ar da kike gudanarwa, to ki tabbatar wannan sana’ar taki zai iya tsayuwa da kafarsa (Karban kudi daga wajen babanki ko saurayinki don zubawa cikin sana’arki ba hikima ba ne).
Sannan fim din ya koyar da mu:
5) Adana, adana, adana, tanadi, tanadi, ajiya (Za ki iya shiga hali na bukatar kudi ta gaggawa);
6) Ki yi adana da tanadi amma fa ki zuba jari (Zuba hannun jari zai zama wani karin hanyar samun kudi ne);
7) Kada ku tsaya dogara da abun da ke hannunku zalla a ci gaba da neman riba (me zai faru idan kudinku ya shiga mashashshara?);
8) Kada ku dogara da kudaden wani ko wasu (Idan sun ba ku to, in sun hanaku ma dai baku dogara da shi ba);
9) Ba za hanyoyin shigar kudi (Zuba jari, kasuwanci daban-daban, buga-bugar nema (Ba shiga harkokin ciwa-ciwo ko yahoo yahoo ba); da kuma na 10 wanda ya kasance mai muhimmanci, ba za ka magance ma wani kalubalen da yake fuskanta na kudi ba.
Fim Din Chief Daddy (2018)
Shi fim din Chef Daddy ya nuna tare da kokarin fita da al’adar kasuwancin dan Nijeriya mai matsakaicin mataki. Kuma kusan a zahirance hakan na faruwa da iyalai da dama.
Bayan mutuwar hamshakin mai kudi ‘Chief Daddy’ (Wadda Taiwo Obileye ya hau kan labarin Chief Daddy a fim din), iyalansa, matansa da ma’aikatansa sun fahimci cewa ba fa za su iya cigaba da rayuwa na alfarma da jin dadi kamar yadda suke yi a lokacin da Chief Daddy yake raye ba.
Darurrsan da Chief Daddy ya koyar wa al’umma:
Kusan dukkanin fim din an dauka ne tare da nuna yadda aka shirya da aiwatar da jana’izar Chief Daddy cikin ban dariya game da rikicin rudewa da rikita-rikitan da iyalai suka shiga ciki.
Bayan sanya burin samun makuden kudade da mutane da makusantansa da dama suka yi.
Sai a karshen fim din aka gano cewa shi marigayin ya yi wasiyyar yadda za a kasafta kadarorinsa da miliyoyin kudaden da ya bari ga iyalansa, kason da za a raba na kasuwancinsa ga iyalansa, da na ma’aikatan gidansa.
Abun takaici da bakin ciki, farin ciki da burin yin arziki daga iyalinsa na neman zama da wuya don kuwa kamar za a iya cewa ga ci ne ga rashi, domin kuwa sun shiga wani matakin da za a iya cewa kudin ahlin mamacin na neman zama na al’umma; tsarin fitar kudin, babu ko mai na kudin da zai fita har sai bayan IPO (International Proposed Organization) ta kammala. Sannu a hankali dai iyalansa suka shiga cikin fatara da talauci. Domin kuwa babu wani Chief Daddy da za su kuma dogara da shi kuma abun da ya tara a duniya ya kasa shigowa hannunsu.
Kamar dai yadda fim din ‘The Smart Money Woman’, ya koyar dangane da muhimmancin tsayuwa da kafafu a bangaren neman kudi. Ta yaya za ka rayu bayan wanda kake samun kudi ko jigonka ya mutu?
Za ka iya cigaba da daukan nauyin rayukarka? Ko kuma za ka fara kwasan kadarorin da ka mallaka domin sayarwa don ka rayu ne? kamar biyan kudin haya, sayen abinci, biyan kudin wuta da sauransu?.
A takaice dai abun da fim din ke koyarwa shine ka nemi sana’a ka dogara da kanka koda kuwa kana cikin daula na dukiya daga wani ko ahlinka. Abu na farko na lura da cewa shin kudin nan da kake rayuwa da shi naka ne? ko kana fakewa da samun wani ne.
Day of Destiny (2021)
Day of Destiny labari ne da shirya kan rayuwar wasu ‘yan uwa biyu Chidi (Olumide Oworu) da Rotimi (Denola Grey) wadanda suka kasance cikin kunci da bakin ciki sakamakon halin matsatsin kudi da iyalansu ke ciki. Suna ta kokarin maida rayuwarsu shekaru 20 baya domin canza hakikanin yanayin rayuwa da suka samu kansu a ciki, amma daga baya sun dawo sun fuskanci yadda rayuwar za ta kasance a nan gaba.
Darasi:
A karshen fim din, bayan da ‘yan uwan suka dawo suka fuskanci hakikanin rayuwarsu, Babansu (Norbert Young) ya fada wa Chidi cewa: “A zahirance mu ba talakawa tukuf ba ne.
Mun sadaukar da jin dadin rayuwarmu ne kawai don kai da dan uwanka da ‘yar uwanka ku samu rayuwa mai kyau mai inganici.” Wannan labarin ya koyar da mu cewa a duk lokacin da dan Nijeriya ya ce ku rayu a yadda kuke, shine mu yi rayuwa daidai karfinmu kuma mu kashe abun da za mu iya.
Ta irin wannan hanyar ne za mu iya yin adana da tanadi domin rayuwarmu ta yi kyau a nan gaba koda kuma za mu shiga yanayi neman kudi cikin gaggawa.
Sugar Rush (2019)
‘Yan uwa uku mata Bola Sugar (Bimbo Ademoye), Sola Sugar (Bisola Aiyeola) da Susie Sugar (Adesua Etomi-Wellington) bisa hatsari kwatsam suka samu dala 800,000.
Kawai suka dukufa amfani da wannan maguden kudaden domin inganta rayuwarsu, suka kama sayen katafaren gida, motocin alfarma, riguna na kawa, shirya liyafa da dai sauransu dukka don holewa.
Cikin rayuwa ta almuzzaranci da wadaka har ta kaisu ga masu mallakin kudin sun sanya zargi a kansu tare da kai su ga hukumar yaki da hancin hanci da rashawa (EFCC), a takaice dai sun fada tarkon hukumar.
Darasin da shirin ke koyarwa:
A cikin wannan labarin na ‘yan uwa mata uku. Sola ita ce ‘yar damfara da ke son yin rayuwa ta karamar yarinya da irin kudin da bata da shi a rayuwa; kan hakan Bola ta dukufa gudanar da rayuwar karya a shafin Instagram; sannan, ita kuma Susie ta fi damuwa da yadda za ta samu kudi domin biyan kudin jinyar mahaifiyarsu da ke fama da cutar Kansa. Duk da hakan, duk da dalilin neman kudi da Susie take ciki, sata a wajenta ya kasance mata matsala.
Abin takaici a garesu, inda suka je satar kudin, an daukesu a hoton daukar hoto. Fim din ya nuna duk halin da mutum zai shiga na kudin rayuwa ya dage ya nemi sana’ar yi kada ya yi sata domin daga karshe za a iya ganoshi kuma rayuwarsa za ta iya shiga garari.
Kuam’s Money (2020)
Fim ne da ya koyar da muhimmanci zuba hannun jari da yadda ake samun riba. Kana ya bada labarin yadda rayuwa ke sauya wa mutum tunani wajen neman sana’a da zuba hannun jari domin samun dumbin riba.
Sannan, labarin ya nuna yadda ake ririta ribar da aka samu da uwar kudin da aka zuba a matsayin hannun jari a wata kamfani domin neman dukiya. Kai tsaye fim din ya koyar da hada-hadar kudi sosai yadda mutum zai yi arziki ta hanyar zuba hannun jari.
Fina-finan Nollywood sun kasance abun so da ban sha’awa lura da halin da ake ciki a halin yanzu na matsatsin tattalin arziki. Abu mai matukar muhimmanci a ciki shine al’umma suna daukan darasi kuma suna koyon yadda za su nemi kudi da muhimmanta shi.