Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya rantsar da sabbin manyan sakatarorin dindindin 13, domin cike guraben da aka samu a ma’aikatun gwamnatin jihar.
Manyan sakatarorin na daga cikin mutane 64, da suka samu nasara bayan fitowar sakamakon jarabawar Kwalejin Gudanarwa ta gwamnatin Nijeriya (ASCON), da mutum 64 daga jihar suka halarta, a watan Nuwambar 2023.
- Amurka Na Daukar Barazanar Da Sin Ke Kawowa A Matsayin Dalilin Fadada Karfin Sojanta A Sararin Samaniya
- Birane 10 Masu Tsadar Rayuwa A Afirka
Sabbin sakatarorin sun hada da Mundi Musa Ibrahim daga karamar hukumar Guyuk, Adama Mamman, daga Hong, Dogara Musa, Hong, Fabian Wambai, Jada, Oliver Gani, Lamurde, da Abubakar Umar, karamar hukumar Maiha.
Sauran su ne Zira Bubanani Mathias, Michika, Kwaji Duguri, Michika, Ruth Huram, Michika, Makallan Akila, Song, Tanimu Buba, Yola ta Arewa, Heidi Edgar Amos, Yola ta Kudu da Muhammad Amin Suleiman Yola ta Kudu.
Da yake jawabi gwamna Fintiri, ya bayyana gudanar da jarabawar a matsayin wata manufa ta karfafa tsarin aikin gwamnati.
Ya ci gaba da cewa “Gudanar da jarrabawar ita ce hanya mafi dacewa wajen samar da ingantaccen tsari domin dakile abubuwan da ke haifar da son zuciya da sauran muhimman abubuwan da suka shafi nada babban sakatare na dindindin,” in ji gwamnan.
Shi ma da yake jawabi, shugaban ma’aikatan jihar, Isah Shehu Ardo, ya bayyana sama da manyan ma’aikata 100, suka nuna sha’awar shiga jarabawar, ya ce mutum 64 daga ciki suka samu zana jarrabawar a watan Nuwamban bara.