A kwanakin baya, wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ta yi hira da firaministan kasar Georgia Irakli Garibashvili dake ziyara a kasar Sin a yayin gasar wasannin daliban jami’o’in kasa da kasa da ake gudanar a birnin Chengdu da ke kudu maso yammacin kasar Sin, inda ya ce, bikin bude gasar wasannin daliban jami’o’in kasa da kasa ta Chengdu yana da nishadi sosai, wanda ya yi kamar bikin bude gasar wasannin Olympics da aka gudanar a baya.
A yayin ziyararsa, Garibashvili ya bayyana yayin da yake ganawa da shugaban kasar Sin Xi Jinping cewa, kasar Georgia ta nuna goyon baya ga shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kiran samun bunkasuwar duniya, da kiran kiyaye tsaron duniya, da kiran kiyaye al’adun duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar. Garibashvili ya ce, wadannan kira suna taimakawa wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa da wadata a duniya, duniya tana bukatar su. (Zainab)