Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang dake ziyara a kasar a birnin Addis Ababa.
Firaminista Abiy ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin ya zabi kasar Habasha a matsayin zango na farko na ziyararsa bayan hawan kujerar mukaminsa, lamarin da ya shaida zumunta mai zurfi da muhimmancin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Ya ce an samu nasarori da dama kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Habasha da kasar Sin a fannonin ayyukan more rayuwa, da tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da aikin gona, da gina yankin raya masana’antu da dai sauransu, wadanda ke da babbar ma’ana, wajen sa kaimi ga raya tattalin arzikin kasar Habasha da sanya ta cikin jerin kasashen dake kan gaba a nahiyar Afirka, kana ya yi maraba da karin kamfanonin Sin da su je kasar Habasha don zuba jari da gudanar da ayyuka.
A nasa bangare, Qin Gang ya bayyana cewa, a cikin fiye da rabin karni bayan kasashen Sin da Habasha sun kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, ko da yake yanayin duniya ya sauya, kasashen biyu sun ci gaba da goyon bayan juna da yin kokari tare, wanda ya zama misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Ya ce kasar Sin ta nuna goyon baya ga kasar Habasha wajen bin hanyar samun ci gaba da ta dace da yanayinta. Haka kuma, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, da sa kaimi ga karin kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar Habasha da shiga aikin sake gina kasar. Qin ya kara da cewa, kasar Sin tana son kasar Habasha ta samar da yanayi mai kyau na yin ciniki da daukar matakai don tabbatar da tsaro da moriyar ma’aikata da hukumomin kasar Sin.
Bugu da kari, minista Qin Gang ya tattauna da manema labarai, tare da mataimakin firaministan Habasha, kana ministan harkokin wajen kasar Demeke Mekonnen, bayan tattaunawarsu a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Da aka nemi jin ra’ayinsa game da yarjejeniyar zaman lafiya ta Habasha da ci gaban da aka samu dangane da shawarar da Sin ta gabatar ta “Makomar Zaman Lafiya da Ci Gaban Kahon Afrika” a Habasha, Qin Gang ya ce, Habasha gida ne na bai daya ga al’ummar kasar, ciki har da mutanen Tigray.
Ya ce kasar Sin ta kasance mai girmama cikakken ikon Habasha da yankunanta, kana tana mara baya ga gwamnatin kasar da al’ummarta, a kokarinsu na cimma zaman lafiya da hadin kai da kuma neman ci gaba.
Da ya yi waiwaye kan ziyarar manzon musamman na Sin a kahon Afrika, Xue Bing ya kai wasu kasashen yankin, Qin Gang ya ce kasar Sin ta goyi bayan babban taron zaman lafiya na kahon Afrika na farko, wanda ya bayar da gudunmawa ga cimma matsaya tsakanin dukkan bangarori da inganta zaman lafiya da ci gaban yankin.
Ya kuma bayyana cewa, Sin ta samar da kashi-kashi na kayayyakin abinci da alluran rigakafi da sauran kayayyakin jin kai ga Habasha, domin taimakawa inganta rayuwar al’ummomin dake yankuna masu fama da rikici.
Dadin dadawa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya fara a wasu kasashen Afirka, jim kadan da kama aikinsa, ta shaida yadda kasar Sin ke darajanta zumuncin da ke tsakaninta da kasashen Afirka, wadda kuma ke da nufin kara dinke zumunci tsakanin sassan biyu.
Wang Wenbin ya ce, bana ce shekara ta 33 a jere, da ministan harkokin wajen Sin ke kai ziyarar aiki ta farko a duk shekara kasashen Afirka.
A ranar 30 ga watan Disamban da ya gabata ne aka nada Qin Gang a matsayin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya kuma fara ziyarar a ranar Talata, inda ya fara da yada zango a kasar Habasha. (Faeza Mustapha, Saminu Alhassan)