A kwanan nan ne, aka rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan game da aikin shimfida layin dogo tsakanin kasashen uku, al’amarin da ya nuna cewa, layin dogon da aka shafe tsawon shekaru ana shirin ginawa zai tabbata. Yayin da yake zantawa da dan jarida na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, firaministan kasar Kyrgyzstan, Akylbek Japarov, ya bayyana cewa, layin dogon da ya hada Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan, zai taimaka ga raya kasarsa, har ta zama mahada dake da makoma mai haske ta fannin jigilar hajoji.
Firaministan ya ce, wannan zai taimaka ga kasar Kyrgyzstan da ma duk yankin tsakiyar Asiya, su zama mahadar kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai wato EU. Haka kuma, ginawa gami da fara amfani da layin dogon, zai sa yankin tsakiyar Asiya ya zama tamkar mahadar mabambantan wayin kai, har ma da zama muhimmiyar mahada ta fannin kasuwanci da jigilar kayayyaki. Kasar Kyrgyzstan za ta yi amfani da wannan kyakkyawar dama tare da taimakon layin dogon, wajen raya kanta har ta zama kasa dake iya jigilar kayayyaki ta hanyar yankin teku. Ya ce wannan shi ne abun da aka aikata a zahirance, a fannin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin-gwiwa da shugaba Xi Jinping ya bullo. (Murtala Zhang)