Firaministan kasar Laos Sonexay Siphandone ya ce kasar Sin ta cimma nasarori sosai a kokarin kawar da talauci a cikin gidanta, ta yadda ta zama abar koyi ga sauran kasashen da suke neman fid da al’ummunsu daga kangin talauci.
Mista Siphandone ya bayyana hakan yayin da yake hira da wakilin CGTN a kwanan baya. Inda ya ce, kasar Sin ta tsara nagartattun manufofi don tinkarar kalubaloli daban daban. Misali, kasar ta sa kaimi ga ci gaban kimiyya da fasaha, musamman ma fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, da gina karin kayayyakin more rayuwa masu inganci, da tabbatar da samun daidaituwa tsakanin larduna da garuruwa daban daban na kasar, a fannin ci gaban tattalin arziki.
- Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata
- Yadda Amarya Za Ta Gyara Jikinta Har Zuwa Ranar Aure (II)
Ban da haka, mista Siphandone ya yabi kasar Sin kan nasarorin da ta samu ta fuskar ci gaban zaman al’umma, da kyautatar muhallin halittu. Ya ce, dukkan birane da kauyukan kasar Sin sun samu babban ci gaba a fannin ingancin muhalli, da yawan yankunan daji, wanda ya dace da tsarin raya kasa da ke farin jini a duniya, wato neman ci gaban tattalin arziki mai dorewa, ta hanyar kare muhallin halittu.
Sa’an nan, dangane da layin dogon da wani kamfanin kasar Sin ya gina, wanda ya hada kasar Laos da kasar ta Sin, mista Siphandone ya ce, layin dogon ya haifar da alfanu sosai, a fannin tattalin arziki, wanda ya zarce yadda aka zata a baya. Kana wannan layin dogon zai zama wani bangaren sabon layin dogon da ya hada kasar Sin da kasar Singapore, wanda za a shimfida shi a nan gaba. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp