Firaministan kasar Sin Li Qiang ya jaddada bukatar zurfafa yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, da kuma tsayawa kan neman ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire, yana mai cewa hakan zai sa kaimi ga bikin baje-kolin hajojin da ake shigowa gami da fitar da su zuwa ketare na kasar Sin, wanda aka fi sani da suna Canton Fair, don ya ci gaba da kara ingantuwa.
Firaministan ya bayyana haka ne a yayin da yake ziyartar rumfar kamfanoni daban-daban a bikin baje kolin na Canton Fair karo na 135 a yau Alhamis, 18 ga wata.
Har ila yau firaministan ya yi mu’amala sosai da ‘yan kasuwa masu sayyaya daga kasashe daban-daban, tare da karfafa musu gwiwar zama gadar inganta hadin kai tsakanin Sin da kasashen waje, da sa kaimi ga samun nasara tare a tsakanin Sin da duniya baki daya. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp