A yau Talata ne, firaministan kasar Sin Li Qiang ya jaddada hadin kai da hadin gwiwa a lokacin da yake jawabi wajen bude taron shekara-shekara na sabbin zakaru karo na 14, wanda ake kira da Davos na bazara, a gundumar Tianjin dake arewacin kasar Sin.
Li ya ce, a cikin shekaru ukun da suka gabata, dukkan kasashe sun yi matukar fafatawa da cutar COVID-19, wacce ta nuna karfin hadin kan dan Adam tare da kula da juna a cikin mawuyacin hali.
Ya kara da cewa, babu wata kasa da za ta zauna lami-lafiya a yayin da ake fuskantar tashin hankali ba tare da ta nemi ɗauki daga sauran kasashe ba. Bugu da kari, bil’adama na fuskantar kalubale a duniya kamar sauyin yanayi, haɗarin bashi, da tafiyar hawainiyar bunkasuwa, da gibin arziki.
Li ya kuma ce, zalunci da wasu nau’in danniya, har ma da yake-yake na cikin gida, da rikice-rikicen yankuna a cikin ’yan shekarun nan, ba kawai sun jawo babbar bala’i ga jama’ar yankunan da abin ya shafa ba, har ma sun haddasa babbar illa ga ci gaban duniya.
Ya kuma bukaci a yi kokarin tabbatar da gaskiya da adalci, da yin aiki tukuru don magance matsalar tsaro, tare da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali don ci gaba.
Sannan firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci taron tattaunawa na ’yan kasuwa, a yayin taron koli na tattauna tattalin arzikin duniya dake gudana a birnin Tianjin, inda ya yi musayar raayi da wakilan ’yan kasuwa.
Darakta janar ta hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, Ngozi Okonjo Iweala da kimanin ’yan kasuwa 120 daga kasashe da yankuna sama da 20 ne suka halarci taron.
Bayan sauraron jawaban da wakilan ’yan kasuwa mahalartar taron suka gabatar, Li Qiang ya ce abun da aka fi bukata a duniya shi ne tuntubar juna da musaya, kuma abu mafi muhimmanci shi ne hadin gwiwa bisa adalci.
Ya ce ba kan ci gabanta kadai ta ke mayar da hankali ba, kasar Sin tana kuma gabatar da damarmakin samun ci gaba ga dukkan bangarori. A cewarsa, Sin kasa ce mai bude kofa, mai tafiya da kowa, kuma sahihiya.
Ya ce a shirye suke su hada hannu da ’yan kasuwa daga mabanbantan kasashe wajen ingiza karin kuzari ga habaka tattalin arzikin duniya. (Masu Fassarawa: Yahaya Babs, Faiza Mustapha)