Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi kira da aiwatar da jerin manufofin da za su daidaita tattalin arzikin kasar.
Li Keqiang, ya yi kiran ne lokacin da ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar a ranar Talata, kwanaki kalilan bayan gudanar da taron koli kan tattalin arziki na shekara-shekara, wanda ya jaddada muhimmancin mayar da hankali kan daidaita tattalin arzikin a badi.
Taron majalisar gudanarwar ta kasar Sin ya bukaci a yi kokarin aiwatar da abubuwan da aka amince da su a taron kolin tattalin arzikin.
Har ila yau, an nanata cewa, za a yi kokarin daidaita ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi da farashin kayayyaki, ta yadda alkaluman tattalin arzikin za su kasance bisa mataki mafi dacewa. (Fa’iza Mustapha)