Firayin ministan kasar Sin Li Qiang ya gana da takwaransa na kasar Kwadibuwa Patrick Achi wanda ya zo kasar Sin don halartar taron shekara shekara na dandalin tattaunawa kan Asiya na Boao na shekarar 2023 a ranar 29 ga watan Maris da ya gabata, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan fannonin da suka hada da aikin gona, da kayayyakin more rayuwar jama’a, da tattalin arzikin zamani da sauransu.
Daga baya firaminista Achi ya zanta da wakiliyar CGTN a ranar 31 ga watan jiya, inda ya yi tsokaci cewa, kasar Kwadibuwa ta bayyana ra’ayoyin kasashen Afirka yayin taron Boao, wanda ruhinsa shi ne hada kai da cin moriya tare. Ya kara da cewa, Afirka nahiya ce mai cike da kuzari, don haka kasashen nahiyar suna fatan za su kara taka rawa kan tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa.
Kana bana aka cika shekaru 40 da kafa huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da Kwadibuwa, mista Achi yana ganin cewa, kasashen biyu sun samu babban sakamako a cikin shekaru 40 da suka gabata, alal misali, kasar Sin ta zuba jari a bangarorin ilmi, da kiwon lafiya, da gina kayayyakin more rayuwar jama’a a kasar ta Kwadibuwa, duk wadannan sun ingiza ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar yadda ya kamata.
Achi ya ce, ya dace a kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a bangarori daban daban, ta yadda za su samu ci gaba tare. (Mai fassarawa: Jamila)