Majalisar zartaswa ta Jihar Kano ta amince da kafa kwamitin mika mulki na mambobi 17 ga gwamnati mai jiran gado a jihar.
Majalisar ta kuma amince da wani karamin kwamiti mai mutum 100 wanda za a fitar da kundin tsarin mulki daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban a jihar.
- EFCC Ta Damke ‘Yan Damfarar Intanet 17 A Benue
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata 2 A Jami’ar Zamfara
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Ya ce kwamitin wanda ke karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Usman Alhaji yana da wadannan mambobi a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnati, babban lauya/kwamishanan shari’a, kwamishinan yada labarai, kwamishinan muhalli, kwamishinan kasuwanci.
Sauran sun hada da kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, kwamishinan kananan hukumomi, kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa, kwamishinan kudi, kwamishinan ilimi da sauransu.
Malam Garba ya bayyana cewa, babban kwamatin zai yi aiki cikin jituwa da nufin mika mulki cikin makonni uku.
Kwamishinan ya bayyana cewa an bai wa babban kwamitin rikon kwarya umarnin fara shirin mika mulki tare da rubuta nasarorin da aka samu a cikin wa’adin mulki biyu na gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Ya ce kwamitin zai kuma samu tare da tantance rahotanni daga ma’aikatu dangane da manyan nasarorin da aka samu, gami da ayyuka da tsari da ke gudana dangane da matakin aiwatar da kasafin kudi, matsaloli da dai sauransu.
Malam Garba ya yi nuni da cewa, an dora wa kwamitin alhakin daidaitawa da gudanar da ayyukan karamin kwamitin kan mika mulki, tattarawa da hada rahotonsu tare da mika rahoton mika mulki ga gwamnati mai zuwa cikin makonni hudu bayan kaddamar da shi.
Ya ce gwamna Ganduje zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata da misalin karfe 2 na rana a dakin taro na ‘Africa House’ da ke gidan gwamnatin Kano.