Firaministan Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif ya bayyana a yayin taron ’yan jarida da aka gudanar a ofishinsa dake Islamabad, babban birnin Pakistan jiya cewa, bangaren Pakistan ya gode wa Sin bisa taimakon kayayyakin agajin da ta samar mata sakamakon ambaliyar ruwa da ta fuskanta.
Yayin da yake amsa tambayar wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua , Shahbaz ya ce, Pakistan da Sin sun dade suna tinkarar kalubale gami da taimakon juna tare. A halin yanzu, Pakistan tana fama da bala’in ambaliyar ruwa mafi muni cikin tarihinta.
Wannan ya sa bangaren Sin ya samar da taimako masu dimbin yawa ga bangaren Pakistan wajen yaki da ambaliyar ruwa da sauran bala’i, lamarin da ya kara karfafa gwiwar al’ummomin Pakistan.
A jiya ne kuma, wani jirgin saman dako kayayyaki samfurin Y-20 na sojojin saman kasar Sin, dauke da kayayyakin shawo kan ambaliyar ruwa da Sin ta baiwa Pakistan, ya isa birnin Karachi dake kudancin Pakistan.
Hukumar kula da bala’o’i ta kasar Pakistan ta bayyana cewa, tun daga tsakiyar watan Yuni zuwa yanzu, mamakon ruwan sama da ya haddasa bala’o’i iri iri a cikin Pakistan, ya haddasa mutuwar mutane 1136, yayin da fiye da miliyan 33.04 suna fama da bala’in. (Safiyah Ma)