Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, na da dama, da ikon amfani da shawarar nan ta inganta jagorancin duniya ko GGI, a matsayin zarafi na taka rawar gani a fannin dora duniya kan turbar kyakkyawan jagoranci. Li ya fadi hakan ne a jiya Talata, yayin taro karo na 24 na shugabannin kasashe membobin kungiyar ta SCO.
Li, ya kara da cewa a watan Satumban bana ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar GGI yayin taron dandalin SCO na birnin Tianjin, wanda hakan ya shaida basirar kasar Sin, da hikimarta ta warware matsaloli, domin taimakawa sassan kasa da kasa da dabarar hada-karfi-da-karfe wajen shawo kan kalubalen gaggawa da na sauyi da duniya ke fuskanta.
Daga nan sai ya yi karin haske game da muhimmancin SCO a fannin ginawa, da kuma aiwatar da sauye-sauye ga tsarin duniya. Ya ce da farko, kamata ya yi SCO ta yi amfani da fifikon karfinta na musamman. Kana na biyu ta mayar da hanhaki kan muhimman sassan samar da ci gaba da tsaro. Na uku kuma, kungiyar ta ingiza karfin farfado da kirkire-kirkire da sauye-sauye.
Firaminista Li ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da daukacin membobin SCO wajen kara lura da muhimman tsare-tsare, da ingiza hadin gwiwa yadda ya kamata, da kyautata, da bunkasa tsarin gudanar da ayyuka, da ma kara zurfafa amincewa juna, da ikon aiwatar da matakai, da tasirin sassanta, da ci gaba da karfafa, da inganta kungiyar ta SCO. (Saminu Alhasan)














