Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya alkawarta fadada bude kofa ga kamfanoni masu jarin waje, ta hanyar kara bude kofar Sin ga daukacin sassan duniya, duk kuwa da sauye sauye da duniya ke fuskanta.
Li, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin zantawarsa da wasu zababbun masu baje hajoji, da masu sayayya dake halartar baje kolin kasa da kasa na kasar Sin, na hajojin da ake shigowa da su kasar ko CIIE karo na 7.
- Kamfanin Google Ya Bai Wa Nijeriya Tallafin N2.8bn Don Bunkasa Tattalin Arziki
- Dole Ne A Gyara Kuskuren Da Tsirarrun Kasashe Suka Yi Na Kiyaye “Dangantakar Diflomasiyya” Tsakaninsu Da Yankin Taiwan
Ya ce duk da tafiyar hawainiya da farfadowar tattalin arzikin duniya ke yi, hada hadar tattalin arzikin kasar Sin na tafiya bisa daidaito tare da samun ci gaba. Kaza lika, kasuwar kasar Sin ta ci gaba da kasance daya daga wadanda kamfanonin kasa da kasa ke zaba.
Firaministan na Sin ya ce kasar sa za ta ci gaba da saukaka harkokin kasuwanci, da ingiza salon fadada bude kofofin ta a sassa daban daban, kamar na sadarwar wayar tarho, da ilimi, da raya al’adu da kiwon lafiya. Yana mai shan alwashin ci gaba da kyautata yanayin gudanar da kasuwanci a kasar.
Daga nan sai ya yi fatan cewa, baya ga kasancewar Sin cibiyar fitar da hajoji ta kamfanonin kasashen waje, za ta kuma zama wuri na zuba jari ga sana’o’i, da ingiza dinkewar Sin da sauran kasuwannin duniya.
A nasu bangare kuwa, kamfanoni masu jarin waje da suka halarci zaman, sun bayyana karfin gwiwar su game da kasuwar Sin, suna masu alkawarta zurfafa hada hadar su da zuba karin jari a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)