Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tattauna da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz dake ziyara a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin Jumma’ar da ta gabata.
Li ya bayyana cewa, kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan alakar dake tsakaninta da kasar Jamus.
Yana mai cewa, a shirye kasar Sin ta ke ta yi aiki da bangaren Jamus, don sa kaimi ga inganta alakar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Jamus, bisa tushen mutunta juna da cin moriyar juna, ta yadda za a kara farfado da tattalin arzikin duniya da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Firaminista Li ya kara da cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, shi ne kashin bayan alakar kasashen biyu, kuma kasar Sin tana fatan karfafa alaka da kasar Jamus a fannoni na cinikayya da zuba jari da masana’antu da yaki da COVID-19, da kara yin hadin gwiwa don daukar matakan da suka dace kan matsalar sauyin yanayi.
A nasa bangare kuwa, Scholz ya bayyana cewa, kasar Jamus ba ta goyon bayan rarrabuwar kai, kuma a shirye Jamus take ta yi aiki da kasar Sin don magance tasirin annobar COVID-19, da zurfafa alaka da saukaka mu’amula tsakanin jami’an sassan biyu, don bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)