Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da tawagar wakilan cibiyar bunkasa cinikayya ta Amurka karkashin jagorancin shugabar cibiyar Suzanne Clark.
Yayin ganawar yau Laraba a birnin Beijing, Li Qiang ya ce a bana ake bikin cika shekaru 45 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka, kuma cikin wadannan shekaru 45 tarihi ya tabbatar da yadda Sin da Amurka suka ci gajiya daga hadin gwiwar su, suka kuma gamu da koma baya sakamakon fito na fito. Don haka hadin gwiwa shi ne kadai zabi mafi dacewa.
A nata bangare kuwa, Clark cewa ta yi alakar Amurka da Sin na da matukar muhimmanci. Kuma raba-gari tsakanin su ba hanya ce mai bullewa ba, kaza lika ana maraba da kara bude kofofin kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)