A yau Asabar ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sauka a birnin Jakarta domin ziyarar aiki a kasar Indonesia bisa gayyatar da shugaban kasar Indonesia Prabowo Subianto ya yi masa.
Li ya bayyana cewa, kasashen Sin da Indonesia sun bayar da misali kan yadda manyan kasashe masu tasowa suke aiki tare don kara karfi da cin moriyar juna da kuma samun nasara ga kowane bangare.
- CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari
- Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF
Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Indonesia don ci gaba da samar da wadata ga al’ummomin Sin da Indonesia ta hanyar tabbatar da makoma guda a tare, da bin hanyar zamanantarwa.
Kazalika, ya ce, a matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa, kuma manyan muhimman kasashe masu karfi a cikin kasashe masu tasowa, ya kamata Sin da Indonesia, su ci gaba da raya ruhin Bandung zuwa mataki na gaba, da karfafa hadin kai da daidaita lamurra, da kuma kara matse kaimi ga tabbatar da aiki da hakikanin tsarin damawa da kasashe daban daban. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp