Firaministan kasar Sin Li Qiang zai gudanar da tattaunawa ta “1+10” a birnin Beijing tare da shugabannin manyan hukumomin tattalin arziki na duniya, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar a yau Jumma’a.
Li zai gudanar da tattaunawar ne tare da shugabar bankin raya ababen more rayuwa a kasashe masu samun ci gaba (NDB) Dilma Rousseff, da shugaban bankin duniya Ajay Banga, da manajan daraktar asusun ba da lamuni na duniya Kristalina Georgieva, da shugabar hukumar cinikayya ta duniya Ngozi Okonjo-Iweala, da babbar sakatariyar babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan ciniki da bunkasa ci gaba Rebeca Grynspan, da shugaban kungiyar kwadago ta duniya Pablo F. Hernandez de Cos, da shugaban hukumar kula da harkokin kudi Andrew Bailey, da shugaban bankin zuba jari kan kayayyakin more rayuwa na Asiya Jin Liqun, kana da mataimakin babban sakataren kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki da bunkasa ci gaba Frantisek Ruzicka, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana.
Kazalika, mai magana da yawun ma’aikatar ya ce, taken tattaunawar shi ne “Yin aiki tare a kan inganta jagorancin duniya domin ci gaba na bai-daya.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)














