Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City mai rike da kofin Firimiya Lig na kasar Ingila za ta karbi bakuncin kungiyar Liverpool a filin wasa na Etihad Stadium dake birnin Manchester.
City ita ce a matsayi na daya akan teburin Firimiya Lig na bana,yayin da Liverpool ke bi mata a matsayi na biyu.
- Ratciffe Na Dab Da Sayen Kashi 25 Na Manchester United
- Bayan Fasa Sayen Manchester United, Sheikh Jassim Na Neman Sayen Tottenham
Akwai yiwuwar zakaran dan wasan Manchester City Erling Haaland ya buga wasan duk da cewar ya samu rauni a kafarsa yayin da yake wakiltar kasar Norway a wasannin kasa da kasa.
Kungiyoyin biyu sun hadu sau 192 a tarihi,inda Liverpool ta samu nasara a wasanni 94 aka yi canjaras 51 sai kuma Manchester City ta samu nasara sau 47.