A karashen tattaunawar da wakilinmu, ADAMU YUSUF INDABO ya yi da marubuciyar yanar gizo, AMINA MA’AJI da muka fara kawo muku a makon jiya ta bambanta marubutan baya da na yanzu bisa fahimtarta, a karanta har karshe amar haka:
To daga 2015 da kika fara rubutu zuwa yau shekaru 8. Kin rubuta littattafai da adadinsu ya kai nawa?
Na rubuta littafi guda Goma Sha Biyu. Da suka hada da Namiji Krin Kunama, Ki Yi Min uzuri, Ni Da Haidar, A Kula Da Mu, Ashe Haka So Yake, Dan Adam Butulu, Aminatu, Halacci Ne, Gidan Marayu, Ina Mafita, ‘Yancin Mata, Zabi Biyu.
To cikin su wanne ne bakandamiyar ki?
Gidan Marayu. Na sha wahala wajen rubuta littafin sannan ya samu karbuwan da ban yi zato ba. Ya jawo mun alkairi da yawa na samu kyau ta da yawa. Duk da ya fi ba ni wahala duk cikin littafan da na rubuta, dan na je gidan marayu kafun in samu ganin masu ruwa da tsaki a cikin gidan na sha wahala, na sha kuka ganin yadda rayuwar marayu yake.
Cikin wanne yanayi da lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?
Na fi jin dadin rubutu a lokacin da nake cikin farin ciki sannan ba ni da wata damuwa, ina son yin typing da dare yana sa in tsai da hankali na wajen yin rubutu a cikin nutsuwa.
To kuma ya batun kungiyoyin marubuta?
Na shiga kungiyoyi guda biyu rashin hadin kai ya sa na fita saboda yawanci ba ma kiyaye dokokin group shi ya sa yanzu bani da wani kungiya guda daya, na shiga Haske da kuma perfect duk na fita Allah ya sa mu dace.
Kasancewar ki tsohuwar makaranciya ya za ki kwatanta marubutan da da kuma na yanzu ta fuskar kwarewa da kuma yin rubutu mai ma’ana?
Na ji dadin tambayar nan. Marubutanmu na da suna rubutu cikin hikima da basira ga labarin yana da ma’ana, sannan akwai darasi cikin sigar dabara sannan ba sa tsananta dogon labari. Na yanzu kuwa sai karyan ya tafi kasar waje a can za a yi rayuwa, alhalin marubuciyar ko nan da Sokoto ba ta je ba, amma za ki ji rubutun ya tafi. Kadan ne daga cikin su masu rubutu irin na da akwai wata marubuciya Badi’at Ibrahim, littafinta duk irin na da ne akwai hikima wajen rubuta shi. Sannan marubutan da ba su da mu da ka’idojin rubutu da yawa ba, na yanzu sukan yi amfani da ka’idojin rubutu. Misali kamar ni da Sadnaf Badi’at mukan rubuta ‘true life story’ ne dan gaskiya in ka ce in rubuta abun da bai faru da gaske ba shirme zan yi. Nakan yi bincike gidaje da yawa masu shigen irin labarin akwai littafi na Halacci ne littafin ya yi duba ga ‘yan shaye-shaye, na sha wahala sai da na je gun yan shaye-shaye cikin hikima tare da siya musu abinci da ruwa da lemo kafin na samu karin haske. Yana da kyau mu marubuta mu dinga yin bincike sosai kafin mu dora alkalaminmu. Allah ya yi mana jagora. Sannan ya kamata mu dinga rubuta labari a cikin jahar mu dan a gane a ina muke.
To daga fara rubutunki zuwa yau. Wadanne nasarori kika cimma ta silar rubutu?
Nasaran farko sanin manyan marubuta na biyu karban award guda daya na uku marubuta sun san ni.
To wanne irin kalubale kika hadu da shi?
Kalubalin da na fuskanta a cikin gida ne, Sam ba sa son in dinga rubutu a nasu fahimtar bata lokaci ne, sai daga baya suka gane rubutu hanya ce na isar da sako cikin hikima. Na biyu rashin hadin kan marubuta shi ke sani damuwa nakan dauki marubuta tamkar jinina amma rashin hadin kai shike damu na, hakika ba ni da kamar marubuci a rayuwata a duk in da marubuci yake ina alfahari da shi koda yau ne ya fara rubuta kalman ‘A’ a matsayin rubutu amma kash abun sai a hankali.
To mece ce shawararki na ganin an dinke wannan baraka ta rashin hadin kan marubuta?
Abu ne wanda za mu ce Allah ya hada kanmu kawai, dan gaskiya sai mun cire hassada kafun haduwar kai zai yi tasiri, mu cire kyashi ga junanmu, mu dauki rubutu a matsayin sana’a.
Wanna buri kike da shi a rayuwa?
Ina son in zama babbar marubuciyar da duk duniya a san ni koda a jahata ne na ci nasara sosai. Burina na biyu ina so mu yi gangamin hada taron marubutan online na kowani jaha a san juna.
A karshe wanna kira za ki yi ga ‘yan uwanki marubuta?
Ina kira ga marubuta yan uwana mu hada kanmu wajen gina gaskiya, sannan kananan marubuta musamman wanda ba su yi aure ba, su daina sako harkan da ta shafi gidan aure baranta na takai ga shimfida, ta kiyaye wannan su tsarkake alkalaminsu, su yi rubutu mai tsafta su ji tsoron Allah, dan in sun yi rubutu cikin rashin hankali zabsu karanta ranan da babu musu.
Wanna sako kike da shi ga masoyanki dake bibiyar dukkan rubuce-rubucenki?
Masoyana a koda yaushe ina alfahari da su. Kuma ni ma ina kaunarku masoyana.