Yusuf Shuaibu" />

FIRS Ta Samar Da Harajin Tiriliyan N4.178 A Watanni 10 – Shugaban Hukumar

FIRS

Hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) ta bayyana cewa, ta samu nasarar tattara harajin da ya kai na naira tiriliyan 4.178 a cikin watanni 10. Shugaban hukumar FIRS, Mista Muhammad Nami shi ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da rahoton harajin cikin gida da aka samu a wajen taron mahukunta haraji karo na 46, wanda ya gudana a garin Abuja. Nami ya bayyana cewa, an samu nasarar cimma kashi 99 na harajin da aka yi tsammanin samu a cikin watanni 10, wanda aka yi tsammanin samun harajin naira tiriliyan 4.230. Ya kara da cewa, a farkon wata ukun shekarar 2020, an amshi haraji daga daukacin jihohin kasar nan guda 36 ciki har da babban  birnin tarayya na naira biliyan  974.197. a cewarsa, an samu karuwar kashi 1.39 idan aka kwatanta da wanda aka amsa a farkon wata ukun shekarar 2019 na naira biliyan 988.024.

“Tabbas cutar Korona ta rage samar da haraji musamman ma a wasu yankuna da ke cikin kasar nan wanda aka tattara harajin shekara a fadin jihohi 36, inda aka sami naira tiriliyan 1.334 a shekarar 2019.

“Mun dauki babban darasi a lokacin cutar Korona wanda ya janyo muka yi amfani da kimiyya da sauran dubaru wajen samun damar tattara harajin shekara a cikin kasar nan.

“Mu na da tabbacin samun goyan bayan masu ruwa da tsaki a bangaren haraji wajen cike gibin da ake samu a cikin haraji a cikin kasar nan,” in ji Nami.

Haka kuma, shugaban hukumar FIRS ya ci gaba da bayyana cewa, a yanzu haka ana shirin gabatar wa jihohi hanyar yadda za su dunga biyan haraji ta na’urar wutar lantarki domin samun saukin biyan harajin. Ya kara da cewa, wannan ne zai sa a saukaka yin amfani da na’urar lissafi da kuma sauran ayyukan haraji ga dukkanin bangarorin gwamnati guda uku. Ya kara jaddada cewa, hukumar FIRS a shirye take da aiwatar da gyara a cikin hanyoyin samun kudade wanda zai amfani Nijeriya.

Exit mobile version