Hukumar tara haraji ta ƙasa (FIRS) ta buɗe hanyoyin neman aiki ga ƙwararrun ma’aikata don cike guraben aiki na musamman a hukumar. A wata sanarwa da ta fitar a kafar sada zumunta ta X (da aka fi sani da Twitter), FIRS ta bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na dabarunta kan inganta ayyukan hukumar.
Guraben da aka sanar sun haɗa da mataimakin manaja da mataimakin darektan haraji (bincike), PRS (bincike), hulɗar jama’a, da ICT (tsaron yanar gizo da gudanarwar AI). Haka nan akwai guraben mataimakin manaja da mataimakin darektan PRS bangaren doka, da kuma manyan manajoji a binciken haraji.
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Aniyar Amurka Ta Sanya Karin Haraji Kan Wasu Hajojin Sin Dake Shiga Kasar
- ASUU Ta Yi Kira Ga Majalisar Kasa Ta Cire TETfund Daga Tsarin Sabuwar Dokar Haraji
Hukumar ta bayyana cewa masu neman guraben aikin dole ne su mallaki digiri ko HND tare da sakamako mai daraja ta biyu (second class lower) ko ƙasa da haka (lower credit). Ya zama tilas masu neman aikin mataimakin manaja da mataimakin darekta su kasance ba su wuce shekara 40 ba, yayin da manyan manajoji da mataimakan darakta ba su wuce shekara 45 ba zuwa 31 ga Disamba, 2024.
An kuma buƙaci masu neman aikin su kasance suna da ƙwarewa a fannonin shugabanci da gudanarwa, haɗin kai, iya ba da aiki ga wasu, da kuma samun ƙwarewa wajen sadarwa da fahimtar dokokin haraji na Nijeriya.
Masu sha’awar aikin na iya ziyartar shafin yanar gizo na FIRS: careers.firs.gov.ng domin cikawa kafin ranar ƙarshe, 11 ga Janairu, 2025.