Fitacciyar mawakiya ta Jamhuriyar Nijar, Hamsou Garba ta rasu a jiya da daddare a wani asibiti da ke Babban birnin kasar Niamey.
Hamsou ta rasu ne tana da shekara 64 bayan ta sha fama da rashin lafiya.
An haifi Hamsou ne a birnin Maradi, kuma ta shafe fiye da shekara 30 tana waka, inji rahoton BBC Hausa.
Ta kasance tana wakar ta ne da Hausa sai ta sirka kadan da faransanci, Wakokinta sun fi mayar da hankali ne a kan soyayya da addini da zamantakewa da gwagwarmayar siyasa da kuma kishin kasa.
Kungiyar mawaka ta kasar ta bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi a fannin waka na kasar,
Ta rasu ne mako biyu bayan rasuwar mijinta da kuma babbar ‘yarta da ita ma ta rasu wata daya da ya gabata.