Allah Ya yi wa shahararren ɗan jarida da ya yi fice a gidajen rediyo, Aliyu Abubakar Getso, rasuwa bayan doguwar jinya.
Kamar yadda iyalan marigayi Getso, suka sanar wanda muryarsa ta kasance abar da aka saba ji kuma ake girmamawa a kafafen yaɗa labaran Arewacin Nijeriya, ya rasu da safiyar yau Lahadi 5 ga Oktoban 2025 a Kano, kuma tuni an yi jana’izarsa bisa tanadin addinin Musulunci.
- Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?
- Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or
A tsawon rayuwarsa ya yi aiki a manyan gidajen rediyo da dama ciki har da Gidan Rediyon Jihar Kano, da Freedom Radio, da Premier Radio da Vision FM, inda ya sami yabo saboda fasaha, ƙwarewa da sadaukarwa wajen hidimar jama’a ta hanyar watsa labarai.
Ya samu yabo musamman a kan ƙwarewarsa a fagen nazari kan al’amuran yau da kullum na cikin gida da ƙasashen waje tare da fahimtar da masu sauraro cikin sauƙi.
Marigayi Getso, ya bar mata uku da ‘ya’ya da jikoki, inda abokai da sauran ‘yan uwa suka bi sahun alhinin rasuwarsa, tare da bayyana hakan a matsayin babban rashi ga fannin yaɗa labarai a Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp