Mawakan Nijeriya kamar sauran gama garin mutane ne, suna bin doka da oda, wanda ka iya sa a kama su ko tsare su ko dai a hannun ‘yan sanda ko kuma a gidan yari idan sun aikata ba daidai ba.
Taurarin Nijeriya da dama sun ci karo da batutuwan shari’a kuma duk da shahararsu, dukkansu sun dauki nauyin gudanar da ayyukansu.
- Idan Ruwan Dagwalon Nukiliya Bai Gurbata Ba, Me Yasa Japan Ba Ta Ajiye Shi Ba?
- Jakadun Kasashen Afirka Sun Bayyana Gamsuwa Ga Makomar Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
A dangane da hakan LEADERSHIP ta ranar Lahadi ta yi la’akari da mawakan Nijeriya 8 da aka kama tare da tsare su kamar haka.
Burna Boy
A shekara ta 2010 an kama Burna Boy saboda wani laifin daba da wuka a Amurka, inda ya ki amsa laifinsa, amma duk da haka sai da ya tafi gidan yari, an sake shi bayan ya shafe watanni 11 yana tsare, kuma sakin nasa ya biyo bayan kyawawan halayensa da ya nuna lokacin da yake gidan yarin.
Mutumin da ya yi kaurin suna a Afirka ya tsere daga Amurka ya dawo Nijeriyaya fara sana’ar waka kafin a kammala sakinsa a Amurka.
Sinzu
An kama Sinzu, wanda aka fi sani da Sauce Kid a Amurka a shekarar 2017, a lokacin da yake shirin shiga jirgi bisa laifin satar sama da Dala 15,000 ta hanyar zamba ta katin banki.
Yana da tsabar kudi Dala 6000 da na’urar da ake amfani da ita wajen tsara katunan banki.
An daure shi na tsawon shekaru 2.
Tems
A cikin Disamba 2020, Tems ta shiga cikin matsala lokacin da aka kama ta a Kampala, Uganda. Kamar yadda rahotanni suka bayyana, an kai ta kurkuku saboda yin watsi da ka’idojin Korona. Tems ta halarci wani wasan kide-kide da aka soke saboda kar a keta dokar Korona da aka aiwatar a wancan lokacin.
Hukumomin tsaro na Uganda sun sanya masu laifin a matsayin masu son kai. Sun ce “sun yanke shawarar karya umarnin Korona. Wannan ya kasance da niyyar samun riba tare da yin barazana ga rayukan ‘yan Uganda da dama a cewar jami’an tsaron kasar.” Sakamakon haka, an tsare Tems da manajanta a hannun ‘yan sanda na tsawon kwanaki biyu kafin a sake su.
Bayan haka, sun dawo Nijeriyaa ranar 17 ga Disamba, 2020. Dangane da lamarin, Tems ta fitar da wata sanarwa inda ta nuna alhininta, tana mai bayyana cewa masu halarta na iya yuwuwar kamuwa da Korona.
Omah Lay
Kamar Tems, Omah Lay shima an an kama shi a Uganda cikin Disamba 2020, lokacin da shi da Tems suka je Uganda don yin wasan.
An yi tsammanin wannan zai zama dare na nishadi da kida ga magoya bayansu, abin bakin ciki, lamarin ya rikide ya zama mafarki mai ban tsoro lokacin da hukumomin Uganda suka kama duka ‘yan wasan biyu bisa zargin karya ka’idojin Korona.
Omah Lay ya yi amfani da kafofin sada zumunta na intanet inda ya nuna rashin jin dadinsa da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa an mayar da shi “kamar barawo.
Mawakin ya bayyana cewa kwanakin da suka gabata na daga cikin mafi wahala a rayuwarsa. Gwamnatin Nijeriyata taka rawa wajen ganin an sako Omah Lay da Tems, wadanda aka tsare su na tsawon kwanaki biyu a hannun ‘yan sanda kafin daga bisani a sake su su dawo Nijeriya.
D’Banj
Shahararren mawakin Nijeriya, D’Banj a watan Disamba 2022, ya shiga hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) tare da tsare shi.
Tauraron mawakin dai an tsare shi ne bayan da jami’an hukumar ta ICPC suka kai samame, suka tilasta masa mika kansa a shelkwatar hukumar da ke Abuja, bisa zargin zamba.
Ana zargin D’Banj da zamba da karkatar da daruruwan miliyoyin Naira da gwamnatin Nijeriyata ware domin gudanar da aikin N-Power, shirin karfafawa da gwamnatin Nijeriya ta kafa a shekarar 2016 domin magance matsalar rashin aikin yi da matasa ke fama da shi da kuma kara bunkasa zamantakewa.
Rahotanni sun bayyana cewa D’banj ya kasance jakadan Brand a ma’aikatar.
An yi zargin cewa mawakin ya hada baki da wasu jami’an gwamnati wajen shigar da masu amfana a cikin tsarin biyan albashin, sannan an biya kudaden alawus din da aka biya wa wadanda suka ci gajiyar kudin a asusun da a yanzu ake zargin an alakanta su da mawakin.
Portable
A ranar Juma’a, 31 ga Maris, 2023, jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun sun kama Portable bayan ya kasa mika kansa duk da cewa an ba shi wa’adi.
An dai dauki hoton mawakin yayin da yake furta kalaman batanci ga jami’an ‘yansanda da suka ziyarci mashayarsa da ke gundumar Sanga Ota a Jihar Ogun domin kama shi.
Ya ki bai wa jami’an hadin kai, inda ya bayyana cewa shi babba ne kuma ba za a iya kama shi ba, rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta gurfanar da Portable a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda biyar da suka hada da cin zarafi, rashin da’a, da satar kayan kida.
A ranar Litinin, 3 ga Afrilu, 2023, alkalin kotun da ke shari’a a garin Ifo, a Karamar Hukumar Ifo ta Jihar Ogun, ya bayar da belin Portable bayan an tsare shi a gidan yari na Ilaro domin cika sharudan belinsa.
A cewar Portable, tsohon ma’aikacin ya je ofishin ‘yansanda ne ya kai kararsa saboda kawai ya yi masa gyara. Ya kare abin da ya aikata da cewa shi ne shugaban koyon kuma ya hore shi ta hanyar dukansa.
Seun Kuti
A watan Mayun 2023, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya umurci kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas da ya kama mawakin Afrobeat, Seun Kuti, bayan an dauki hotonsa a wani faifan bidiyo yana cin zarafin dan sanda sanye da kayan aiki.
Wata kotun majistare da ke zaune a Yaba a jihar Legas, ta bayar da umarnin tsare mawakin Afrobeat a hannun ‘yan sanda na tsawon sa’o’i 48 don bai wa ‘yan sanda damar kammala bincike kan zargin cin zarafi da aka yi masa.
Alkalin kotun, Adeola Olatunbosun, wanda ya jagoranci lamarin, ya kuma umurci ‘yan sanda da su saki mawakin bayan wa’adin da aka kayyade a kan beli, sannan kuma ya aika da takardar karar zuwa ofishin kula da kararrakin jama’a (DPP), domin a ba da shawarar lauya.