Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni shidan farko na bana, an kafa sabbin kamfanoni 30,014 na masu zuba jari daga kasashen waje a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna karuwar hakan da kashi 11.7 cikin dari a mizanin duk shekara.
Kazalika, bayanai sun nuna cewa, saka hannun jari daga kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ya karu da kaso 8.8 cikin dari a tsakanin lokacin.
Har ila yau, jarin da aka zuba daga kasar Switzerland ya karu da kaso 68.6, na Japan ya karu da kashi 59.1, na Birtaniya ya karu da kaso 37.6, sai kuma na Jamus da ya karu da kashi 6.3, kana wanda aka zuba daga Jamhuriyar Koriya kuma ya karu da kashi 2.7 bisa dari. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp