Masana a fannin noman rogo a kasar nan sun bayyana cewa, daga cikin tan miliyan 53 na rogon da ake noma wa a Nijeriya a duk shekara, fiye da kashi 90 cikin dari ana sarrafa shi zuwa sauran wasu nau’ukan abinci.
Kididdga ta tabbatar da wannan adadin, inda masanan suka kara da cewa, fannin na noman Rogon ya taimaka wajen samar wa da miliyoyin ‘yan Nijeriya aikin yi idan kuma aka inganta fannin, zai samar fiye da hakan.
Masanan sun sanar da hakan ne a a taron kara wa juna sani da suka gudanar a Babban Birnin Tarayyar Abuja, inda kuma suka yi nuni da cewa,kokarin da gwamtin tarayya ke ci gaba da yi na sake farfado noman na rogo a Nijeriya, musamman kan daukain da Babban Bankin Nijeriya CBN ke samar wa a fannin, inda ya yi nuni da cewa, CBN ya bayar da gagarumar gudunawa wajen bunkasa fannin na noman rogo a kasar nan.
“Kokarin na gwamtin tarayya a fannin abin yaba wa ne matuka, musamman ganin cewa, nomansa na daya daga cikin amfanin gona da ke kara karfafa tattalin arzikin duniya”.
A cewar masanan, Nijeriya ce ke kan gaba wajen noman rogo, inda suka bayyana cewa, kasar na samar da kimanin tan miliyan 53 na rogo a shekarar 2018 tare da kuma ta ke samar da akalla tan 7.7 ako wacce kadada daya, idan aka kwatanta da tan 23.4 da kuma tan 22.2 da ake samarwa a kasashen in Indonesiya da Thailand.
Masanan sun sanar cewa, ci gaba da sake farfado noman na rogo a Nijeriya da gwamnati ke ci gaba da yi, musamman ta hanyar yin amfani da daukin da kan Babban Bankin Nijeriya ya kara taimaka wa matuka wajen kara bunkasa fannin na noman rogon a kasar, da kara fitar da shi zuwa kasuwar duniya, inda kuma hakan ya kara samar wa gwamnatin kasar kudaden shiga masu dimbin yawa.
“Nijeriya ce ke a kan gaba wajen noman rogo, inda suka bayyana cewa, kasar na samar da kimanin tan miliyan 53 na rogo a shekarar 2018 tare da kuma ta ke samar da akalla tan 7.7 ako wacce kadada daya, idan aka kwatanta da tan 23.4 da kuma tan 22.2 da ake samarwa a kasashen in Indonesiya da Thailand”.
Masanan sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi dukkan mai yuwa wajen kara samar da masu zuba jari a fannin na noman rogon a kasar, musamman idan aka yi la’akari da irin dimbin kudaden shiga da fannin ke samar wa da manoman rogon a kasar, inda kuma suka yi yi nuni da cewa, hakan zai kara taimaka wa wajen kara samar da ayyukan yi ga “yan kasar nan, musamman matasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp