Kamfanin LEADERSHIP ya bi sahun sauran kamfanoni don karfafa hadin gwiwar kafofin yada labarai ta hanyar wani shiri na musayar ra’ayi da nufin inganta hadin gwiwar Sin da Afirka don samun moriyar juna.
An tabbatar da hakan ne a wani biki mai taken “Wayewa da gina mafarkanmu a nan gaba: ‘Hadin gwiwa da Afirka’ wanda rukunin kamfanin yada labarai na kasar Sin (CMG) ya shirya a Babban birnin kasar, Beijing, a ranar 31 ga Agusta, 2024, gabanin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) a birnin Beijing.
- UNECA: Sin Na Tallafawa Afirka Sauyi Zuwa Makamashi Mai Tsabta Ta Hanyar Shigar Da EV
- An Kaddamar Da Shirin “Afirka a Cikin Fina-Finai” Zagaye Na Biyu
An fara taron na FOCAC ne a ranar 4 ga watan Satumba kuma za a kammala shi a ranar 6 ga watan Satumba.
Tun lokacin da aka kafa FOCAC a shekarar 2000 da asusun raya kasar Sin da Afirka a shekarar 2006, dangantakar tattalin arzikin kasar Sin da Afirka ta zurfafa sosai.
Taron kafofin watsa labarai kuma shine don haɓaka musayar al’adu da koyan juna a cikin zamani na dijital.
Taron ya samu halartar mutane fiye da 200 da suka hada da wakilai daga kungiyoyin kasa da kasa da kafofin yada labarai da jaridu da kungiyoyin tunani da sauran bangarori na kasar Sin da fiye da kasashen Afirka 20.
Shugabannin kasashen Afirka da dama da suka hada da shugaban kasar Uganda, Yoweri Kaguta Museveni; shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera da shugaban Seychelles, Wavel Ramkalawan, sun mika sakonnin su ta hanyar bidiyo inda suka bayyana goyon bayansu ga inganta mu’amalar kafofin watsa labarai da hadin gwiwa a zahiri tsakanin Sin da Afirka.