An kaddamar da shirin koyar da Sinanci mai taken “Hello China”, na gidan rediyon Nijeriya (FRCN), a Abuja babban birnin kasar. Kusan mutane 100, ciki har da jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai da darakta janar na FRCN Mohammed Bulama ne suka halarci bikin kaddamarwar da ya gudana a jiya Alhamis.
Cikin jawabin da ya gabatar, Yu Dunhai ya ce kaddamar da shirin na koyar da Sinanci da gidan rediyon ya yi, zai samar wa ‘yan Nijeriya wani sabon dandali na koyon harshen Sinanci da fahimtar kasar Sin, tare da samar da kuzari mai dorewa ga hadin gwiwar moriyar juna a fannonin cinikayya da tattalin arzikin tsakanin Sin da Nijeriya
Daga ranar 16 ga wata ne za a fara watsa shirin na “Hello China” a fadin kasar, a kowacce ranar Laraba daga karfe 5 zuwa 5:30 na yamma. Shirin ya kunshi koyar da harshen Sinanci da karin haske game da ilimin tattalin arziki da kimiyya da zaman takewa da al’adun kasar Sin. Ana sa ran shirin zai zama wata sabuwar kafa da ‘yan Nijeriya za su samu cikakkiyar fahimta ta ainihin kasar Sin daga bangarori daban daban. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp