Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2024 ga ‘yan majalisar dokokin jihar na tsaginsa su biyar.
Hakan ya biyo bayan yadda aka wayi gari da rushe ginin majalisar dokokin jihar.
A kwanakin baya ne ‘yan majalisar 27 suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
‘Yar majalisar 27 da ke biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ba su halarci zaman gabatar da kasafin kudin ba.
Alaka dai ta yi tsami tsakanin Fubara da uban gidansa Wike, wanda har a baya sai da shugaba Tinunu ya shiga tsakani domin yi musu sulhu.
A baya wasu tsagin ‘yan majalisar jihar sun kokarin tsige gwamnan, sai dai a wannan karon ma ba ta sauya zani ba ganin yadda suka ki halartar taron gabatar da kasafin kudin shekarar mai zuwa na jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp