Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere daga gidan gyaran hali na Kotonkarfe da ke Jihar Kogi da safiyar ranar Litinin, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba.
Kwamishinan YaÉ—a Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce an sake kama É—aya daga cikin fursunonin da suka tsere.
- Dokar Ta-ɓaci A Ribas: Gwamnonin PDP Sun Ƙalubalanci Hukuncin Tinubu A Kotun Ƙoli
- Kamfanin Apple Ya Sanar Da Zuba Sabon Jari A Fannin Samar Da Makamashi Mai Tsafta A Sin
Fanwo ya bayyana cewa gwamnatin jihar na aiki tare da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu nasarar tserewa ba tare da an gansu ba.
Ya ce dole ne a gudanar da bincike mai zurfi domin gano musabbabin lamarin da kuma kama waÉ—anda ke da hannu a ciki.
Ya ce abin mamaki ne yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba, don haka dole ne a zaƙulo masu hannu a lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanai da za su taimaka wajen kamo sauran fursunonin da suka tsere.
Haka kuma, an buƙaci dangin waɗanda suka tsere da su mika kansu ga hukuma domin guje wa hukunci mai tsanani.
Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan matsala ba, domin a baya an samu fursunoni sun tsere daga gidajen yari daban-daban a Nijeriya.
Hakan na nuni da buƙatar ƙara tsaurara matakan tsaro a gidajen gyaran hali domin hana faruwar irin haka a gaba.
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da bincike tare da ƙoƙarin kamo sauran fursunonin da suka tsere domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp