Hukumar gyaran hali ta ƙasa (NCoS), reshen Jihar Kano, ta karrama ɗalibai 62 da suka samu nasarar yin jarrabawar kammala Sakandire (NECO) da kuma madadinta ta ƴan arabiyya (NBAIS).
Taron karrama ɗaliban ya gudana a cikin shirin ci gaba da karatu na ‘yan gidajen yari, wanda wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta rayuwar fursunoni da kuma shirya su sake shiga cikin al’umma don zaman masu amfani bayan sun bar gidan gyaran.
- Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara
- An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin shekaru 2 A Gidan Yari Saboda Yunƙurin Daɓa Wa Mahaifinsa Almakashi A Kano
A cikin wata sanarwa daga Jami’in hulɗa da Jama’a na reshen hukumar a Kano Kano, CSC Musbahu Nassarawa, an bayyana cewa wannan shiri yana cikin tsarin dokar hidimar gyaran hali ta Nijeriya ta shekarar 2019, wanda ke ƙarfafa samun damar ilimi na yau da kullum da horon sana’o’i ga ‘yan gidajen yari don taimaka musu wajen dawowa cikin al’umma.
A cikin jawabinsa a lokacin taron, Kwamandan hukumar na Jihar Kano, Ado Inuwa, ya yaba da ƙoƙarin Kwamanda Janar na hukumar gyaran hali ta ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, wajen ba da kulawa ga lafiyar ‘yan gidajen yarin.
Inuwa ya kuma yaba wa Gwamna Abba Yusuf da gwamnatin Jihar Kano kan tallafin da suke bayarwa wajen samar da damar ilimi ga ‘yan gidajen yarin, inda ya jaddada cewa wasu daga cikin ɗaliban da suka kammala sun samu nasarorin jarrabawa a muhimman fannonin ilimi kamar harshen Ingilishi da Lissafi.
A ƙarshe, wakilin Gwamna Abba Kabir Yusuf a taron, Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Faruk, ya nuna jin daɗinsa da ci gaban da aka samu wajen gyaran ɗaliban ta hanyar ilimi na yau da kullum, yana tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen ilimi na ‘yan gidajen yari a matsayin muhimmin mataki na dawo da su cikin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp