Wata babbar kotun Jihar Ekiti da ke Ado Ekiti ta yanke wa Daudu Jimoh mai shekaru 62 hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara tara fyade a Ilupeju Ekiti.
An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Lekan Ogunmoye a ranar 5/8/2020 bisa tuhumar aikata laifin fyade.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon-Gaba Da Jami’an Lafiya Da Marasa Lafiya A Jihar Neja
- Hukumar Shige Da Fice Ta Shirya Wa Jami’anta Gwaji Kan Shan Miyagun Kwayoyi Da Horo Na Musamman A Yenaguwa
A cewar mai shigar da kara, “Daudu Jimoh a ranar 27/9/2019 a Ilupeju Ekiti da ke cikin ikon wannan kotun mai martaba ya yi wa yarinya ‘yar shekara tara fyade, hakan ya saba da sashe na 31 (2) na dokar kare hakkin yara, Cap. C7, na dokokin Jihar Ekiti, na 2012.
“A shaida ta gaban kotu, wadda aka azabtar ta ce, “Na halarci makarantar Firamare da ke Ilupeju Ekiti, sau hudu yana lalata da ni kafin kanwata ta kama mu a wata rana a tsaka da hakan.
“Duk lokacin da ya yi lalata da ni, na kan ji tsoron gaya wa mahaifiyata domin ya gargade ni kada na sake na fada wa kowa in ba haka ba zan mutu,” in ji ta.
Domin tabbatar da kararsa, mai gabatar da kara, Julius Ajibare, ya kira shaidu hudu tare da gabatar da bayanan wadanda ake tuhuma da kuma rahoton likita a matsayin shaida yayin da wanda ake tuhuma ya yi magana a kan kare kansa ta hannun lauyansa, Chris Omokhafe, ya ce ya aikata laifin amma ya musanta cewa ya shiga cikin farjinta.
Lokacin da ya ke yanke hukuncin, mai shari’a Lekan Ogunmoye, ya ce, ikirari na wanda ake tuhumar, a rubuce da kuma ta baka, ya nuna ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, cewa lallai wanda ake tuhuma ya aikata laifin.
An yanke masa hukunci duba da karancin shekarun wadda ya yi wa fyaden.
”An yanke masa hukuncin daurin rai da rai,”cewar alkalin kotun.