Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala sayen Gabriel Jesus daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, kamar yadda kungiyar ta bayyana a safiyar yau bayan an kammala gwada lafiyar dan wasan a satin daya gabata.
Tun farkon bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ne dai aka danganta dan wasan, dan Brazil da komawa Arsenal, sakamakon daukar dan wasan gaba, Erling Haaland, da Manchester City ta yi wanda zai hana shi samun damar buga wasanni akai-akai.
- Gwamnatin Zamfara Ta Fara Horas Da ‘Yan Sa-Kai Don Yakar ‘Yan Bindiga
- PDP Reshen Jihar Osun Ta Koka Kan Yadda ‘Yan Sanda Ke Yi Wa ‘Ya’Yanta Dauki Dai-dai
Dan wasan mai shekara 25 zai saka riga mai lamba 9 a sabuwar kungiyar tasa, kuma ya bayyana cewa sun tattauna da kocin Arsenal Mikel Arteta, wanda shi ne ya ja hankalinsa, ya amince da komawa kungiyar da ke birnin Landan.
Jesus wanda ya shafe shekara biyar da rabi a Manchester City ya buga wasanni 236 sannan ya zura kwallaye 95 a kungiyar tun bayan komawarsa daga Palmires a 2016, sannan ya lashe kofi 11 ciki har da gasar Firimiya guda hudu.