Ganawar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni na jam’iyyar PDP ciki har da Nyesom Wike a Landan ta kada hantar Jam’iyyar PDP.
An dai bayyana cewa gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da takwaransa na Jihar Abiya, Dakta Okezie Ikpeazu da wasu jiga-jigan PDP suna daga cikin tawagar Gwamna Wike wajen taron ganawar.
Wata majiya ta bayyana cewa Wike da wasu magoya bayansa ciki har da Gwamna Samuel Ortom na daga cikin wadanda suka garzaya Landan domin gudanar da tattaunawar sirri.
Idan za a iya tunawa dai, tun bayan da Gwamna Wike ya sha kaye a zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP suka shiga takun-saka da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abukabar. Duk da kokarin da masu ruwa da tsaki suka yi wajen sulhunta su, amma lamarin ya ci tura, wanda har magoya bayan Wike sun dage sai shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya sauka daga kan mukaminsa.
Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar za ta bayar da hankali ne kan Wike da magoya bayansa su mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC baya. Rahotannin dai na nuna cewa ana kokarin cimma matsaya ne kan ko Wike zai dawo APC ko kuma zai yi wa Tinubu aiki daga jam’iyyarsa ta PDP a zaben shugaban kasa na 2023.