Daraktan Janar na yada labarun Gwamnan Jihar Zamfara, Nuhu Salihu Anka ya bayyana cewa ganawar sirin da tsofaffin gwamnonin Jihar Zamfara guda 4 suka yi a gidan karamin ministan tsaro, Bello Matawale, ba kan batun tsaro ba ne, siyasarsu ce ta sa suka gana domin su wawantar da hankalin mutane.
Nuhu Anka ya bayyana haka ne a lokacin da wakilinmu ya tambaye shi karin haske kan taron ko sun sanar da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal kan samun shawarwari.
- Shalƙwatar Tsaro Ta Karyata Rahoton Sace Mutane 500 A Zamfara
- Gwamnan Zamfara Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Daga N7,000 Zuwa N30,000, Za A Fara Biya Daga Yuni
Ya dai ce taron da suka yi na siyasa ce, amma sakatare yada labarai na APC na Jihar Zamfara ya maida shi na tsaro.
Ya ce da Allah ya ta shi bayyana gaskiyar lamari, sai ya sanya a rahoton sakataren yada labarai na APC a Jihar Zamfara na karshe ya kawo batun hadin kan siyasar APC, mai ya kawo hadin kan siyasa a batun harkar tsaro? Wannan shi ne abun tanbaya.
A cewarsa, a kwanan baya Gwamna Dauda ya kaddamar da rundunar Askarawan Zamfara, wanda tsohon gwamna, Ahmad Sani Yariman Bakura ne kadai ya zo taron, kuma daga baya ba su ji sun yi taro domin taimaka wa shirin Askawaran ba wajen yakar ‘yan ta’addan, sai yanzu da APC ke neman wargajewa.
Idan za a iya tunawa a ranar 19 ga wannan watan ne tsofaffin gwamnonin Jihar Zamfara hudu da suka hada da Sanata Ahmed Sani Yarima da Mamuda Aliyu Shinkafi da Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da kuma karamin ministan tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle suka gudanar da wata ganawar sirri domin tattauna hanyoyin inganta harkokin tsaro a jihar da ke ci gaba da tabarbarewa.
Haka Kuma sun tattauna batun ci gaban jam’iyyar APC a Jihar Zamfara da yadda za ta samu hadin kai.