Ana rade-raden cewa, shugaba Bola Tinubu yafi nutsuwa da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin wanda yafi dacewa ya maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
Jaridar Solacebase ta rahoto, an samu labari a daren Laraba cewa, an cire sunan Ganduje daga jerin sunayen ministocin Tinubu.
Majiyoyi sun bayyana cewa, Tinubu ya gamsu sosai da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar.
A halin yanzu dai gwamnonin jam’iyyar APC na zaman taron sirri domin tattauna halin da jam’iyyar ke ciki.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron da ke gudana a masaukin gwamnan jihar Imo da ke Asokoro Abuja, sun hada da gwamnan mai masaukin baki kuma shugaban kungiyar Gwamnoni, Sanata Hope Uzodinma (Imo); Dapo Abiodun (Ogun); Umar Bago (Nijar); Francis Nwifuru (Ebonyi); Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara); Mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Ayedatiwa; Fr. Hyacinth Alia (Benue), Uba Sani (Kaduna); Babajide Sanwo-Olu (Lagos); Mai Mala Buni (Yobe); da Dikko Radda (Katsina).